
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin sama da maniyyata miliyan 1.5 ne suka je Saudiyya daga wajen ƙasar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, lamarin da ke nuna adadin ya haura na bara duk da yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rikicin wanda aka fara a ƙarshen watan Fabarairu tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, ya shafi wani sashi na Saudiyya da wasu sassan yankin Gulf, wanda ya janyo tsaiko ga sufurin jiragen sama da tsadar tafiye-tafiye.
Manyan tashoshin jiragen sama a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Ƙatar da Bahrain sun yi aikin gyara harkokinsu cikin hanzari makonni bayan rufe su.
Duk da waɗannan matsaloli da ake fuskanta, maniyyata daga sassa daban-daban na duniya sun garzaya Saudiyya domin sauke farali a Hajjin bana.
Haka kuma, adadin maniyyatan bana da suka je ƙasar daga waje ya kai guda 1,518,153, kamar yadda kwamandan bada fasfon hajji na Saudi, Saleh Al-Murabba ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a.
A shekarar da ta gabata ne adadin mahajjata ya kai 1,673,320 da suka haɗa da guda 1,506,576 daga wajen Saudiyya.
