
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen mawaƙin nan na Nijeriya, Davido ya sake tayar da hazo a kafafen sada zumunta, inda ya bayyana adadin kuɗaɗen da yake karɓa a kowace gayyata.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ƙwararren mawaƙin na ‘Afrobeats’, ya ce ba ya karɓar ƙasa da Dala 600,000 a kowane aikin gayyata, wato kimanin Naira miliyan 825 gwargwadon matakin sauyin kuɗi.
Davido ya bayyana cewa, aƙalla yana amsar gayyata guda huɗu a kowane wata, wanda ya kai jimillar kuɗaɗen da yake samu a wata zuwa Dala miliyan 2.4, wato biliyan N3.4.
Wannan batu ya janyo gagarumar cece-kuce tsakanin masoya da masu amfani da Soshiyal Mediya, inda wasu ke bayyana mamakinsu akan maƙudan kuɗaɗen da ake samu a masana’antar nishaɗi.
Wasu na nuna yadda waƙoƙin Afrobeats suka faɗaɗa a matakin duniya, wanda ya kai ga mawaƙan Afirka na gogayya da mawaƙan ƙasa-da-ƙasa wajen cazar kuɗaɗen gayyata.
