Bindow ya janye shiga takarar gwamnan Adamawa a ADC, ya jaddada biyayya ga jam’iyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Muhammed Umaru Jibrilla Bindow, ya sanar da janyewa daga shiga takarar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Bindow ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da kuma yin la’akari sosai, inda ya ce janyewar ta samo asali ne daga dalilai na ƙashin kai.

Duk da janyewar, tsohon gwamnan ya sake tabbatar da cikakken biyayya da goyon bayansa ga jam’iyyar, tare da alƙawarin cigaba da mara mata baya da shugabancinta a Jihar Adamawa.

Haka kuma ya yi godiya magoya bayansa, abokan siyasa, da al’ummar Adamawa bisa ƙarfafawa da goyon bayan da suka ba shi a tsawon tafiyarsa ta siyasa.

Kazalika, ya buƙaci magoya bayan nasa da su kasance cikin kwanciyar tare da cigaba da jajircewa wajen haɗin kai da nasarar jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027 da ke ƙaratowa.

By Babaji