Ɗan majalisa ya tallafa wa al’ummarsa don rage fatara

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A wani mataki na ƙarfafa wa da kuma tallaffa wa al’ummar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela dake a Jihar Sakkwato, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela a Majalisar Tarayya, Abdullahi Balarabe Salame ya raba kayayyaki ga al’ummar da yake wakilta na maƙudan nairori.

A cewar ɗan majalisar wannan ya zama wajibi domin rage wa al’umma raɗaɗin talauci da suke fama da shi.

Salame ya ƙara da cewa tallafi ba shakka ya zama tilas kasancewar matsalar talauci da kuma rashin aikin yi ya jefa al’umma cikin ayukkan assha.

Shi ma da yake magantawa shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato Alhaji Bello Aliyu Goronyo ya yaba wa ɗan majalisar da wannan hangen nesan duba da irin halin da al’ummar ƙasar nan ke ciki.

Kayan da aka raba

A kan haka shugaban jam’iyyar ya yi kira ga sauran ‘yan majalisu da su yi koyi da wannan aikin alheirin domin cigaban jiha dama na jam’iyyar musamman a zaɓen shekara 2023 dake tafe.

Aƙalla mutane 50 ne suka amfana da babura 25 da kuma injinan ban ruwa guda 33 kazalika da Keke Napep guda 4.