Addu’a ce takobin dukkan ayyukan ta’addanci – Falakin Ƙaraye

Daga DAUDA USMAN a Legas

An bayyana cewar gudanar da addu’o’i na musamman kan zaman lafiya ita ce takobin kowane irin ƙalubale da ke addabar Nijeriya.

Alhaji Bature Ƙaraye kuma Falaƙin Ƙaraye, mazaunin Legas shi ne ya bayyana haka bayan kammala ɗaurin aurensa a Kano, inda aka yi addu’ar nema wa Nijeriya zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani.

Taron ɗaurin auren dai ya gudana ne a Masallacin Sheikh Jaafar da ke Unguwar Ɗorayi a cikin birnin Kano, inda ya samu halarta manyan baƙi da nesa da na kusa, haɗi da shuwagabannin majalisar Kasuwar Mile 12 da ke Legas irinsu Alhaji Alhaji Isah Mohammed Mai Shinkafa da tsohon shugaban Mile 12 Alhaji Haruna Mohammed Tamarke mai Dankalin Turawa da Alhaji Habu Faki (Garkuwan Faki).

Sauran sun haɗa da: Abdulwahab Tsoho Babangida da babban Shugaba Mai Kulawa da Cigaban Kasuwancin Tumatur a Legas, Alhaji Abdulgayyisu Sani Rano da Alhaji Sabo Magaji Ƙaraye ɗaya daga cikin abokan Alhaji Bature Karaye da sauran waɗansu shuwagabannin ɓangarorin kasuwar baki ɗaya.

Bayan kammala taron addu’o’in guda biyu ne malamai magada Annabawa da sauran shuwagabannin kasuwar ta Mile12 waɗanda suka samu halartar wajen taron addu’ar guda biyu kuma suka yi tsokaci, sun karkata ne a wajen sanya wa Alhaji Bature Falaqin Ƙaraye albarka da sauran ‘yan kwamitin da suka shirya wannan taro.

Da ƙarshe Alhaji Bature Falaƙin Karaye ya isar da saƙon godiyarsa ga Allah da kuma malaman da ya gayyata suka gudanar da waɗannan addu’o’i guda biyu da shuwagabannin kasuwar ta Mile12 da sauran ɗumbin al’ummar da suka zo taya shi murnar gabatar da wannan al’amari.

Ya nuna jin daɗinsa dangane da irin karamcin da ɗumbin jama’ar suka yi masa, inda kuma ya roƙi Allah Ya saka wa kowa da alheri tare da zaunar da Nijeriya lafiya da kawar da dukkan ƙalubalen tsaron da ke addabar ƙasar.