Uba da ɗansa sun rasa ransu bayan sun faɗa rijiya a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wani magidanci ɗan shekara 60, Malam Bala tare ɗan sa Sunusi Bala, mai shekaru 33 sun faɗa wata tsohowar rijiya da ke Sabon Garin Bauchi, a ƙaramar hukumar Wudil, da ke cikin garin Kano, inda suka rasa rayukansu kafin a kai ga cetosu.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya tabbatar da mutuwar su ranar Laraba da ta gabata a Kano, inda ya ce uba da ɗan nasa sun rasu ne yayin da suke  ɗibar ruwa a rijiya.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata da safe.

“Mun samu kiran gaggawa daga ofishin hukumar kashe gobara na Wudil, da misalin ƙarfe 11: 30 na safe, cewa uba da ɗan sa sun faɗa rijiya.

“Nan take muka tura jami’an mu domin ceto su,” inji Saminu Abdullahi.

Sanarwar ta tabbatar da cewa an samu nasarar fito da su daga rijiyar, amma jim kaɗan bayan fito da su, suka ce ga garinku nan.