Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Adam Namadi, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ya buƙaci wakilai da su mayar masa da naira miliyan 2 da ya basu jim kaɗan kafin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazaɓar Kaduna ta Arewa na majalisar wakilai, wanda ya faɗi a ranar 22 ga watan Mayu.
A cewar rahotanni, Adam, wanda ya yi alƙawarin ƙara Naira miliyan 1.5 a cikin kuɗaɗen da aka ware wa kowane wakilai, ya samu mafi ƙarancin ƙuri’u na ’yan takara uku. Wakilan sun karɓo miliyoyin Naira na Nijeriya daga hannun ’yan takarar da ke zawarcin shugabanci.
Samaila Suleiman wanda shi ne wakilin gundumar a yanzu ya lashe zaɓen inda ya doke Adan Namadi da Shehu Usman ABG.
Suleiman wanda a kwanakin baya ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP, ya doke Shehu Usman ABG wanda ya samu ƙuri’u 14 da ƙuri’u 22.
Wakilan da suka shiga zaɓen fidda gwanin, kamar yadda aka bayyana, sun bayyana cewa, Suleiman ya biya ne tsakanin Naira miliyan 3.5 zuwa N4 ga kowane wakili, yayin da ABG ya fitar da tsabar kuɗi Naira miliyan 2.5, Adam Namadi kuma ya raba Naira miliyan 2 ga wakilai.
