Dubun wasu masu garkuwa ta cika a Kaduna

Daga WAKILINMU

Jami’an Sashen Binciken Sirri na Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya (IRT), sun damƙe wasu ’yan ta’adda biyu bisa zargin yunƙurin garkuwa da fyaɗe a Jihar Kaduna.

Abdurahman Lolo da Muhammed Sani sun shiga hannu ne a yankin Bandoko bayan da suka shiga gidan wani magidanci suka yi garkuwa da shi.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Kaduna, CSP Muyiwa Adejobi, ya ce waɗanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun yi shirin su yi garkuwa da magidancin sannan kuma su yi wa mai ɗakinsa fyade.

Tawagar jami’an ƙarƙashin jagorancin DCP Olatuniji Disu, sun samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne bayan da aka gaya wa rundunar Operation Puff Adder abin da ya faru.

A cewar Kakakin, ’yan ta’addan sun shaida musu cewar niyarsu ita ce su kama magidancin sannan bayan haka, su taru su yi wa matarsa fyaɗe.

“A ranar 29 ga Afrilun 2022 da misalin ƙarfe 11.30 na dare, wasu ’yan ta’adda sun kai hari wani gida a Bandoko da zummar yi wa wata mata fyaɗe bayan sun yi garkuwa da ita. Da alama ‘yan ta’addan suna bibiyar matar wadda ta ke sayar da fura da nono kafin harin.

“Bayan sun fasa ɗakin matar sun shiga suka tarar da ita da maigidanta a kwance, daga nan suka sake lalen shirinsu na garguwa da fyaɗe zuwa garkuwa don neman fansa, sannan suka buqaci maigidan ya miaa musu mabuɗin babur ɗinsa.

“Bayan haka, sai suka buƙace shi ya tuɓe tufafinsa inda suka yi amfani da su wajen rufe masa ido kana suka ɗaure masa hannuwa ta baya. Sannan suka ɗauko babur ɗinsa suka ɗauke shi suka gudu da shi zuwa dajin Gbadoko,” inji Kakakin.

Ya ci gaba da cewa, “bayan ɓarayin sun tafi ne sai surukar matar ta yi ihun neman ɗauki lamarin da ya sa jama’a suka fito amma aka rasa wanda ya iya bin sawun varayin saboda tsoron wataƙila suna ɗauke da makamai.

“Nan da nan ‘yan ƙauyen suka haɗa kan ’yan bangan yankin don bai wa jama’a kariya sannan suka sanar da jami’an tsaro abin da ya faru.

“Bayan da ‘yan sanda suka isa yankin ne ’yan bangan suka nuna musu hanyar da ɓarayin suka bi, daga nan su kuma suka bi sawun.

“Jami’an sun iya gano maɓoyar ɓarayin a dajin Gbadoko da misalin ƙarfe 5 na asuba na ranar 30 ga Afrilun 2022. Ganin ‘yan sanda ke da wuya, ’yan ta’addan suka rantama a na kare suka bar magidancin tare da babur ɗinsa da suka sato.

“Bayan wani lokaci jami’an sun samu nasarar kama ɗaya daga cikin ɓarayin mai suna Abdulrahman Lolo, daga bisani wani mai suna Mohammed Sanni shi ma ya shiga hannu,” inji CSP Adejobi.

Jami’in ya ce, duka su biyun da aka kama sun tabbatar wa ‘yan sanda sun aikata laifin da ake zarginsu da shi, kuma suna cigaba da taimaka wa ’yan sanda da muhimman bayanai.

Da ya ke yi wa ‘yan sanda bayani, Abdurahman Lolo ya ce, “ni da wani Abubarka Baya makiyaya ne a ƙauye guda. Abubakar ne ya buaaci in raka shi zuwa wata rugar Fulani da ke kusa.

“Shirinmu shi ne mu yi garkuwa da wata mata don mu yi mata fyaɗe, amma daga baya shirin ya sauya zuwa yin garkuwa da maigidan matar don neman fansa.

“Tocila da adda da kuma sanduna su ne abubuwan da muka riƙe amma babu bindiga. Waɗanda muka kai harin tare akwai Sani da Abubakar da kuma Umar. Kuma dukkanmu yaran Alhaji Lolo na Gadam Mallam-Mamman ne.

“Sauran abokaina da na ambata sun saba zuwa sata, amma wannan shi ne karon farkon da aka tafi da ni. Aikin da aka ɗora mini shi ne lura da hanya da tura bayanai ga abokanmu da suka tsere a lokacin da ’yan sanda suka fafare mu,” inji Abubakar.
Magidancin da lamarin ya rutsa da shi, Jibril Saidu, ya ba da labarin yadda lamarin ya faru kafin zuwan jami’an tsaro.

A cewar Jibril Saidu, “wani gungun mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka shiga mini gida suka haska mini tocila a ido wanda hakan ya hana ni ganin wuri da kyau. Sun yi barazanar kashe ni da iyalina muddin ban ba su haɗin kai ba.

“Sun tilasta ni tuɓe tufafina kana suka karɓe mubuɗin babur ɗina. Sai suka yi amfani da tufafin nawa wajen ɗaure mini fuska da hannuwana ta baya.

“Sai suka ja ni suka fita da ni sannan suka ɗauke ni a kan babur ɗin nawa suka ƙara gaba. Daga bisani jami’an IRT suka kuɓutar da ni,” inji magidancin.