Jarman Hadejia, Alhaji Abba Sambo ya kwanta dama

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Aal’ummar masarautar Haɗejia sun tashi a cikin yanayi na jimami a ranar Talata biyo bayan rasuwar Jarman Haɗejia, Alhaji Abba Sambo.

Alhaji Abba Sambo Dattijo ne mai shekaru sama da 70 a duniya wanda ya shafe shekaru masu yawa yana kan karagar mulki tun bayan rasuwar mahaifinsa.

Marigayin ya yi fama da ciwon koda wanda haka tasa ake masa wankin ƙoda a Asibitin Kwararru na AKTH.

Bayan dawo da shi Haɗejia cikin wannan makon ya ci gaba da karɓar magani a Babban Asibitin Haɗejia, inda a ranar Talata ya ce ga garinku nan.

An yi masa Sallar janaza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a babban masallacin Juma’a na Hadejia bayan kammala Sallar Azahar da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana, daga nan aka kai shi makwancinsa.

Al’ummar gari sun yi wa marigayin shaida da mutum ne mai haƙuri gami da kyawawan halaye a halin rayuwarsa.

Ya zuwa haɗa wannan labari, Masarautar Haɗejia ba ta fitar da sunan wanda zai gaji sarautar marigayin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *