Hattara da masu son raba kan ‘yan Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A daidai lokacin da na ke wannan rubutu, rahotanni na bayyana cewa an samun asarar rayuka da ɓarnatar da dukiya ta ɗimbin Naira, a sakamakon wani rikici da ya ɓarke a wata kasuwar sayar da kayan gine-gine da ke DeiDei a Babban Birnin Tarayya Abuja, tsakanin ‘yan kasuwa ɓangaren Hausawa masu aikin acaɓa da ɓangaren ‘yan ƙabilar Ibo masu sayar da kayan aikin gini.

Wannan na zuwa ne, bayan mummunan abin Allah wadai da ya faru a Jihar Sakkwato na ɓatancin da ake zargin wata ɗalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato Deborah Samuel ta yi wa shugaban halitta Annabi Muhammad (SAWA). Abin da ya tunzura ɗalibai Musulmi da ke makarantar suka yi mata kisan gilla da ƙone-ƙone. Daga bisani kuma wata zanga-zanga ta ɓarke a cikin garin Sakkwato biyo bayan kama wasu ɗalibai biyu da ake zargi da hannu a kisan da aka yi wa Deborah, don neman a sako su, ba tare da an hukunta su ba.

A sakamakon haka rahotanni sun ce wasu ɓata gari da suka shiga cikin matasan da ke wannan zanga-zangar da aka fara ta cikin tsari da lumana sun shiga fasa shagunan ‘yan ƙabilar Ibo da wasu wuraren ibadar Kiristoci wato Coci-Coci, domin huce haushin ɓatancin da da ake zargin waccan xialiba ta yi Annabin Rahama. Abin da ya haifar da sanya dokar hana zirga-zirga ta tsawon awoyi 24 a cikin garin Sakkwato da kewaye, domin daƙile wannan tarzoma da ta tashi.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i cikin tasa hikimar ganin abin da ya biyo bayan zanga-zangar Sakkwato ya kafa dokar hana duk wata zanga-zanga a duk faɗin jihar, domin hana wasu mutane fita titi don nuna goyon baya ko nuna rashin jin daɗi na abin da ya faru, wanda a dalilin haka komai na iya faruwa, saboda da tarihin da jihar ke da shi na samun rikice-rikice tsakanin Musulmi da Kirista.

Waɗannan abubuwa da suke faruwa a ɗan tsukin wannan lokaci ba masu daɗin ji ba ne, domin kuwa a daidai lokacin da ake shirye shiryen gudanar da Babban Zaven 2023, ‘yan siyasa a shirye suke su kawo wani abu na saɓani da zai ƙara raba kan ‘yan Nijeriya don cimma wasu muradun su na siyasa. Don haka komai ƙanƙantar abu sun san yadda za su ɗaukake shi a kambama shi ya zama babba. Ballantana kuma maganar addini da ta taɓa zuciyar kowanne musulmi.

Ba yau ne ake samun saɓani tsakanin Hausawa da Inyamurai ko ‘yan ƙabilar Ibo a wasu sassan ƙasar nan ba, musamman a duk lokacin da aka samu wani rikici mai nasaba da addini da siyasa, amma a wannan lokacin ya fi muni da haifar da tsoro da fargaba, duba da cewa ba ‘yan ƙabilar Ibo ne ake zaman doya da manja ba, har ma da sauran waɗanda ba musulmi ba, da ke nuna jin zafin su kan abin da ya faru a Sakkwato.

Babu mamaki, lokacin da aka samu rahoton fashewar kurtun sinadarin gas a shagon masu aikin walda da ke ƙasan ginin wata makarantar yara a unguwar Sabon Gari da ke Kano, wanda ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, nan da nan aka fara yaɗa jita-jitar cewa bam ne Hausawa suka saka a unguwar ‘yan ƙabilar Ibo, domin dai a nuna cewa za a samu rikicin addini da na ƙabilanci a Arewa.

Abin takaici ne yadda wasu ɓata gari a cikin ƙasa ke ta ƙoƙarin shirya maƙarƙashiya don ganin an haifar da wata damuwa tsakanin ‘yan Arewa da Kudu ta fuskar addini da siyasa, domin ganin ƙasar ta dagule ko ta rabe biyu. Za mu iya fahimtar hakan daga yadda jim kaɗan da faruwar waƙi’ar Sakkwato, aka samu wasu da suka fitar da wani saƙo da ke cewa Majalisar Dattijan Arewa ta fitar da wani jawabi da ke nuna buƙatar a kori ‘yan Kudu daga Arewa kuma a ba su damar kafa ƙasar su da suka daɗe suna nema, zargin da Kakakin ƙungiyar Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ƙaryata da cewa, sam ba su yi wata magana mai kama da haka ba, kuma ba sa goyon bayan angiza wasu su ɗauki doka a hannu ko korar ‘yan wani ɓangare daga Nijeriya.

Wakilan gwamnati, sarakunan gargajiya, malaman addini, ‘yan siyasa da ‘yan boko na da hakkin wayar da kan mabiyansu ta hanyar amfani da kalamai na hankali da suka dace da doka, domin tausasa zukatan talakawa da ƙarfafa gwiwar su ga sauke nauyin da ke kansu a matsayin su na ‘yan ƙasa nagari, wakilan al’umma ko jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Waɗannan irin labarai na jita-jita ko na ƙanzon kurege za su cigaba da bayyana daga ɓangarori daban-daban, ta inda muke tunani har da da ta inda ba mu taɓa tsammani ba. Domin kawar da hankalin ‘yan Nijeriya daga wasu muhimman batutuwa da ya kamata su mayar da kai a kansu don samar da shugabanni nagari. Wasu ire-iren waɗannan bayanai nada matuƙar haɗari ga cigaba da zaman lafiya da haɗin kan ƙasar nan. Musamman batutuwa da suka shafi addini da ɓangaranci, abubuwa masu matuƙar tasiri a zukatan ‘yan Nijeriya.

Ya kamata mu yi hattara kuma mu lura da mu kiyaye daga irin waɗannan abubuwan da za su riƙa bijirowa don a harzuƙa mu mu ɗauki doka a hannu ko mu tayar da tarzoma don wasu baragurbin ‘yan ƙasa ko ‘yan siyasa su cimma muradun su. Abin da ya faru a Abuja ko a Sakkwato abubuwa da za a iya kauce musu, amma saboda jahilcin wasu da yadda aka gurvata tunanin wasu ‘yan Nijeriya aka sanya masa ƙyamar juna da rashin ganin martaba da mutuncin bambance-bambancenmu, ya haifar da mummunan martani, har aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.

Dole ne mu riqa kai zuciya nesa, a yi aiki da hankali, domin tantance abin da ya ke daidai da wanda ba daidai ba.

Allah ya ba mu zaman lafiya, ya ba mu fahimtar juna, da shugabanni na gari.