Zaɓen fidda gwanin PDP: Mahadi ya janye wa Dauda Lawal

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

‘Yan sa’o’i kafin zaɓen fidda gwani a takarar gwamna a jihar Zamfara ƙarƙashin Jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa a yau Laraba, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Barr. Mahadi Aliyu Gusau, ya janye daga takarar shi tare da goyon bayan Dr. Dauda Lawal Dare.

Mai taimaka wa tsoho Mataimakin Gwamnan a kafafen watsa labarai, Hon. Umar Game Game ne ya bayyana haka a wata hira da Jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho ranar Laraba.

Game Game ya bayyana cewa, tsohon mataimakin gwamnan ya janye takararsa tare da goyon bayan Dr. Dauda Lawal Dare bisa umarnin da mahaifinsa, Janar Aliyu Muhammad Gusau ya ba shi.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewar, Janar Gusau wanda ya yi aiki a matsayin Mataimakin Shugan Ƙasa ta fannin tsaron ƙasa a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya zamanto jigo a Jam’iyyar PDP ba kawai a jihar Zamfara ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.

Barr. Mahadi ya yi kira ga dukkan magoya bayansa musamman wakilan da za su gudanar da zaɓen fidda gwanin, da su zabi Dr. Dauda Lawal Dare a lokacin zaɓen fitar da gwanin da zai gudana.

Dr. Dauda Lawal Dare tsohon ma’aikacin banki ne a ƙasar nan.

By Editor