Ɗan takarar jam’iyya mai mulkin Ghana ya amsa shan kaye a zaɓen Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasar Ghana kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NPP ya sha kaye a zaɓen da aka kammala a ranar Lahadi inda ya taya tsohon shugaban ƙasar, John Mahama murna bisa nasarar da ya samu.

A wani jawabi da Mista Bawumia ya gabatar, ya tabbatar da nasarar da jami’iyyar adawa ta NDC a mataki na shugaban ƙasa da na ƴan majalisu ta samu.

Ya kuma yaba da zaɓen kasancewar an gudanar da shi cikin lumana tare da karɓar shan kaye da ya yi.

Mahama wanda ya sha kaye a hannun Nana Akufo-Addo a shekarar 2016, zai fara jagorancin shugabancin ƙasar ne a watan Janairun 2025.

By Babaji