‘Yan bindiga sun sace mata sama da 50 a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Kakin Dawa da ke ƙarƙashin gundumar Gidan Goga a ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mata sama da 50.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Musa Lawali Kakin Dawa ya shaida wa wakilin mu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun yiwa ƙauyen ƙawanya da misalin ƙarfe 1 na daren jiya inda suka fara bincike gida-gida.

“Lokacin da suka afkawa ƙauyen, yawancin mazaje sun gudu domin tsira da rayukan su, saboda mun san cewa mu ne abin da suke nema, amma sai muka gano cewa sunyi awon gaba da matan mu sama da 50 da safe bayan mun dawo gidajen mu”.

Ya ƙara da cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da ‘yan mata da matan aure.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su kawo musu ɗauki tare da turo jami’an tsaro a yankin da za su yaƙi ‘yan bindigar domin a samu zaman lafiya a yankin.

“Muna kira ga hukumomi da su duba halin da muke ciki ta hanyar tura jami’an tsaro a yankin mu domin daƙile waɗannan ‘yan ta’addan da ake fargaba saboda rayuwarmu na cikin haɗari sosai a halin yanzu .

Sai dai ƙoƙarin wakilin mu yayi na jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Asp. Yazid Abubakar hakan bai samu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi