Daga IBARAHIM MUHAMMAD a Kano
Ɗaya daga dattawan Arewa, Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass, ya yi kira ga masu madafun iko akan su sani cewa wa’adin zaɓarsu a wa’adin mulki ba ya wuce shekaru huɗu, ‘don haka su ji tsoron Allah su tsaya suyi abinda ya dace domin sauƙaƙawa al’umma halin ƙunci da ake ciki a ƙasar nan.
Ya ce, “idan aka bari shekaru huɗun suka tafi a wahala ya za a yi kenan Ina zan a yi da dimukraɗiyya dole a gyara yanzu ga irin abinda ya faru a ƙasar Nijar maƙociyar mu azaba ce ta yi wa mutanen ƙasar yawa soja suka karɓi mulki mutane suka nuna musu goyon baya.”
ɗanpass ya yi nuni da cewa “har akaso a kawo fitina tsakanin Nijar da Nijeriya Allah kare ya kawo basira aka zauna aka sasanta dole a yi amfani da hankali akai zuciya nesa a zauna a yi gyara kar a riƙa daka ta Turawa da suke haɗa mana fitintunu mu shiga wahala.
“Don haka ya kamata shugabanni su tsaya su kula da da kyautata harkar tsaro da inganta tattalin arziƙi da samar da aikin yi saboda tun daga rufe kan iyaka da gwamnatin baya ta yi rashin aikin yi ya ƙaru na sama da mutum miliyan 20 aka hana masana’antu da arziƙimmu ci gaba.”
Gambo ɗanpass ya shawarci gwamnatin Jihar Kano da cewa maimakon manyan ayyuka da ake a duba me harkar kasuwanci da masana’antu suke ciki a Sharaɗa da Bampai da Challawa a kamfanoni nawa ne suke a rufe da na sauran gwamnoni na Arewa a dawo a gyara a ga yadda za a ciyar da al’umma gaba.
