Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya buƙaci duka ma’aikatan babbar Jami’ar Jihar Nasarawa mallakar gwamnatin jihar su tabbatar suna cigaba da bai wa sabuwar Shugabar Jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman cikakken goyon baya don bata damar cigaba da kawo canje-canje masu ma’ana a jami’ar kamar yadda take yi a yanzu.
Sanata Abdullahi Adamu ya yi kiran ne a jawabinsa a wajen wani babban taron karramawa wadda duka ma’aikatan jami’ar suka shirya don karrama sabuwar shugaban nasu Farfesa Sa’adatu Hassan Liman wacce ta cika kwanaki 100 akan kujerar mulki aka gudanar a babban ɗakin taro na jami’ar a ƙarshen makon da ya gabata.
Ya ce ba shakka kiran ya zame wajibi don idan ana buƙatar ɗorewar ɗimbin nasarori da sabuwar shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta cimma cikin waɗannan kwanaki 100 kacal dole ne ma’aikatan jami’ar baki ɗaya su ci gaba da tallafa mata musamman ta bata cikakken goyon baya koyaushe.
Sanata Abdullahi Adamu ya kuma bayyana zuwan Farfesa Sa’adatu Hassan Liman makarantar a matsayin ceto wa jami’ar inda ya ce daga rahotanni da yake samu a matsayinsa na wanda ya kafa jami’ar a lokacin da yake kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa duk sun tabbatar cewa kawo yanzu Farfesa Sa’adatu Hassan Liman tana cigaba da cimma burin kafa jami’ar wato samar da ingantaccen ilimi irin na zamani wa ɗalibai baki ɗaya inda ya buƙace ta ta cigaba da hakan.
Sanata Abdullahi Adamu ya kuma yaba wa hangen nesa da waɗannan ma’aikatan jami’ar suka yi na shirya taron karrama shugabar nasu Faresa Sa’adatu Hassan Liman don cika kwanaki 100 akan mulki inda ya ce tabbas hakan zai ƙara mata ƙwarin gwiwa ya kuma ƙara mata ƙwazon cigaba da samar wa jami’ar da dinbin nasarori kamar yadda take yi a yanzu.
Ita ma a nata ɓangaren da take jawabi shugabar jami’ar farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta godewa duka ma’aikatan jami’ar dangane da taron karramawar da suka shirya mata inda tayi alkawarin cigaba da yin duka mai yuwa wajen kai jami’ar mataki na gaba a fannin nasarori.
A jawabansu daban-daban suma wasu daga cikin ma’aikatan jami’ar da suka shirye tareda gudanar da taron karramawar wa shugabar su duk sun bayyana cewa sun yanke shawarar yin haka ne don ƙarfafa ta tare da bayyana mata ƙarara cewa sun amince da salon shugabancin ta a jami’ar kawo yanzu wato cikin kwanaki darin inda suka kuma bukace ta ta cigaba da hakan.
Daga cikin abubuwa da aka gudanar a wajen babban taron sun haɗa da bai wa shugabar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da Sanata Abdullahi Adamu da sauran manyan baƙi da suka halarta lambobin yabo na musamman game da muhimman gudunmawa da suke bayarwa wajen inganta yanayin karatu a jami’ar da sauransu.
