2023: Fitattun ’yan takarar da ke zawarcin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alamu sun nuna gangar siyasar 2023 ta fara zaƙi, inda masu sha’awar ganin sun gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya a zaɓen mai ƙaratowa na 2023 sai ƙara wasa wuƙarsu irin ta siyasa suke yi ta fuskar kwarzanta kai da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a sha’anin siyasa. Blueprint Manhaja ta yi nazarin wasu fitattun ‘yan takarar neman kujerar Shugaban Ƙasar Nijeriya da suka fito daga jam’iyyu daban-daban, kamar haka:

Yan takarar APC:

Yemi Osinbajo
Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari’a na Jihar Legas ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya ce, ya tsaya takara ne domin inganta rayuwar ‘yan ƙasar, yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa yana da ƙwarewar shugabancin Nijeriya.

“A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban ƙasa, na wakilci qasar nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin ƙananan hukumomin Nijeriya. Na je kasuwanni, da masana’antu, da makarantu da gonaki,” in ji Farfesa Osinbajo.

Ya ƙara da cewa ya je gidajen talakawan ƙasar a yankuna daban-daban, sannan “na tattauna da ƙwararru a vangaren fasaha a Legas, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaƙa daga Legas da Onitsha da kuma Kano. Kuma na yi magana da ƙanana da manyan ‘yan kasuwa”.

Osinbanjo mai shekaru 65, ya ce ya samu wannan ƙwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolin Nijeriya da kuma yadda zai magance su.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana aniyar tsayawa takararsa ne a wani faifan bidiyo da aka fitar kwanan nan a kafafen talabijin da na sada zumunta.

Bola Tinubu
“Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ƙasa, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya saɓa da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokuraɗiyya, don haka dole mu tafi a kan haka.”

Bayan sanar da takarar tasa, akwai lokacin da ya fito yana shaida wa matasan Najeriya cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.

Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama. “Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?”

“Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,” in ji Tinubu.
Tun a bara ne hotunan takarar Tinubu suka fara karaɗe wasu jihohin Najeriya.

Har yanzu dai bai fito ta kafofin yada labarai kai-tsaye ya yi wa al’ummar Najeriya jawabi kan neman kujerar shugabanci da kuma manufofi ko abubuwan da zai yi idan ya yi nasara.
Amma ana ganin ana iya samun takun saka tsakanin Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osibanjo a neman kujerar mulki.

Rotimi Amaechi
A ƙarshen makon jiya ne Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, mai shekaru 56, shi ma ya fito ya sanar da aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a zaven 2023.

Amaechi ya ayyana takararsa ne a wani taron siyasa a garin Fatakwal a ranar Asabar.

Ya ce: “Na tsaya a gabanku don bayyana aniyata tare da gabatar da buƙatar zama shugabanku na gaba”. Rotimi, wanda tsohon gwamnan Ribas ne, ya ce akwai ɗimbin ƙalubale da ake fama da su a Nijeriya kuma burinsa shi ne share wa ‘yan ƙasar hawayensu.

Ministan da ke bayani kaitsaye ta shafinsa na Facebook ya ce abubuwan da zai mayar da hankali idan ya yi nasara su ne tsaro da rashin ayyuka da yaƙar talauci da kuma haɓɓakar tattalin arziki.

Ameachi ya ce ya shafe shekaru 23 yana siyasa don haka yana da ƙwarewar da ake buƙata kuma nan ba da jimawa ba zai soma gangami a kowane kusurwar ƙasar kama daga birni har zuwa ƙauyuka.

Sanar da matsayarsa da Mista Amaechi ya yi ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da aka shafe watanni ana yi kan cewa yana neman maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi)
Matashin gogaggen ɗan siyasa a Nijeriya, kuma mai sha’awar gadon kujerar Shugaba Buhari a 2023 a ƙarƙashin tutar APC, shine mafi ƙarancin shekaru a APC cikin maza masu neman kujerar zuwa yanzu bayan Gwamna Yahaha Bello na Jihar Kogi.

Ɗan Ƙabilar Kanuri ne a Jihar Borno. An haife shi 3 ga Yuni, 1972 a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Dr. El-Daby ya taso a Jihar Filato inda ya yi mafi yawancin rayuwar shi da karatun shi a jihar. Ya fara karatun firamaren Mishan ta Roman Katolika da ke garin Girin a jihar ta Filato, daga nan ya wuce makarantar sakandiren sojoji dake Zaria (Chindit Barrack).

Bayan ya kammala ya samu shiga makarantar School of Accountancy and Management Studies a garin na Jos, sai kuma makarantar American Academy of Project Management, inda daga nan ya wuce Israila don faɗaɗa karatun shi a Jami’ar Cornerstone, bayan ya kammala, bai tsaya nan ba ya halarci cibiyar International Security Organization Kilgore, wacce take da haɗin gwiwa da mashahuriyar makarantar nan ta ƙasar Indiya wato School of Profiling and Graphology, Sannan ya je ƙasar Kenya inda ya yi karatu a Kwalejin Pan-African Shield Collage dake ƙasar.

Matashin ɗan siyasar mai jini a jika, ya mallaki kwalayen karatu da kwasa-kwasai daban-daban, sannan ƙwararre ne a fannin siyasa da ilimin sha’anin tsaron ƙasa da sanin tattalin arziki.

Shi ne shugaban gidauniyar Almajirai Empowerment Foundation, gidauniyar ta yi fice a faɗin Nijeriya wajen tallafa wa almajirai da mabuƙata.

El-Dabi ya bada gagrumar gudunmuwa wajen kawar da gwamnatin Jonathan da ɗora ta Shugaba Buhari a 2015 da 2019.

Ya riqe muƙamin sakatare na ƙasa na mata da matasa masu yi wa Buhari yaƙin neman zaɓe a 2019. Kuma mamba ne na ƙungiyar magoya bayan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a zaɓen 2019.

Haka zalika ya riƙe Daraktan gudanarwa na magoya bayan Buhari a 2019, wato BSO a taƙaice.

Shi ne Kwadineta na ƙungiyar magoya bayan Buhari daga 2014 zuwa 2015. Sannan mamba a babban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da sa ido kan lamuran zaɓe a 2014.

Ya kuma riƙe sakatare na ƙasa na ƙungiyar Buhari Support Group Center (BSGC) 2014. Sannan mamba a kwamitin shirya babban taron Jam’iyyar CPC a 2013. Da dai sauran muƙamai da dama a siyasa waɗanda suka yauƙaƙa kyakkyawar alaƙarsa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Dr. Ibrahim Bello Dauda (El-Dabi), yana da ƙwarewa da gogewa wajen sanin hanyoyin tsaro da aikata miyagun laifuka, tare da binciken ƙwa-ƙwaf a matsayin sa gogaggen akanta kuma masanin tattalin arziki da sarrafa kuɗaɗen ƙasa da sanin hanyoyin bunƙasa saka hannayen jari a duniya baki ɗaya.

Yahaya Bello
Yahaya Bello kusan shi ne mafi ƙarancin shekaru cikin mutanen da suka fito zuwa yanzu ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC suna neman mulkin Nijeriya.

A ranar 2 ga watan Afrilu, Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa, ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.

Bello ya yi alƙawarin cewa zai mayar da ‘yan Nijeriya miliyan biyu masu arziki da za su mallaki miliyoyi nan da 2030.

Ya ce ya fahimci cewa ci gaban Nijeriya ya dogara ne da fitar da ‘yan ƙasar daga talaucin da ya yi katutu.

Gwamnan ya yi fice wajen yawan shirya taro da mu’amala da masu harkar fina-finai a Nijeriya. Sannan yana cikin na gaba-gaba da ke yi wa Shugaban Ƙasar Muhammadu Buhari biyayya.

Sai dai masana na ɗiga ayar tambaya kan ƙwarewarsa, musamman duba da ci gaban da za a zo a gani a jiharsa Kogi.

Ahmed Sani Yariman Bakura
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara mai shekaru 62, kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa shi ma ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023.

Sanata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin ƙasar ya yi watsi da tsarin karɓa-karɓa a zaman abin da ya sava wa kundin tsarin mulkin ƙasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin ƙasar ya fitar da shugaban ƙasa na gaba.

Ya ce dama sun ɗaga wa Shugaba Buhari ƙafa ne a 2007, kuma a yanzu tun da wa’adinsa ya ƙare lokaci ya yi da zai fito a kara da shi.

Sanatan ya ce ya san matsalolin ‘yan Nijeriya na talauci da jahilci, kuma shi zai mayar da hankali wajen yaƙar waɗannan abubuwa biyu.

Ya ce matsalolin tsaron da ake fama da shi duk saboda rashin ayyukan yi ne, don haka zai bijiro da tsare-tsaren da za su sauƙaƙa wahalhalun ‘yan Nijeriya.

Rochas Okorocha
Tun cikin watan Janairu tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekaru 59, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a babban zaɓen 2023.

Ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, inda shi kuma ya karanta wasiƙar a zaman majalisar.

Okorocha wanda ɗan jam’iyyar APC ne mai mulkin Nijeriya, na cikin ‘yan kudu maso-gabashin ƙasar da ke bayyana aniyarsa ta yin takara a APC.

Rochas ya yi fice wajen ayyukansa na agaji musamman a jihohin arewacin Nijeriya. Sai dai kawo yanzu bai fito ya zayyana manufofi ko abubuwan da zai kawo ba idan ya yi nasara a manufarsa.

Orji Uzor Kalu
Tsohon Gwamnan Jihar Abiya kuma Sanata a Majalisar Dattijan Nijeriya Orji Kalu ya ce ya shirya tsaf don yin takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Orji Kalu na da shekaru 61 a duniya.
Da yake magana da manema labarai lokacin sanar da anniyarsa cikin watan Janairu, Sanata Kalu ya ce ya yi imanin “lokaci ya yi da yankin Kudu maso gabas zai samar da shugaban ƙasa”.

Ya ƙara da cewa zai ƙalubalanci Bola Ahmed Tinubu, Bayerabe kuma ɗan yankin Kudu maso Yamma wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar, idan APC ta amince ta bai wa yankin Kudu takarar.

“Ba na kallon takarar Tinubu a matsayin wani cikas game da yunƙurin ƙabilar Igbo na samar da shugaban ƙasa,” in ji Mista Kalu. “Saboda muna magana ne kan makomar Nijeriya.

Yan takarar Jam’iyyar PDP:

Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma ɗaya daga jiga-jigan mutanen da suka kafa jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce mutane ne suka buƙaci ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwamban 1946 a Jihar Adamawa, jigon ɗan siyasa ne kuma hamshaƙin attajiri a Nijeriya.

Tun bayan da Nijeriya ta dawo mulkin dimokuraɗiyya a 1999, Atiku ya kasance mataimakin shugaban ƙasar na 11, a mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo a tsakanin 1999 zuwa 2007. Ya mallaki katafariyar Jami’ar ABTI, wato American University of Nigeria a jiharsa ta Adamawa.

Kamfaninsa na hada-hadar man fetur, mai suna Intels Nigeria Limited na hada-hada a ƙasashen Afirka da suka haɗa da Angola da Equatorial Guinea da Gabon da Sao Tome da kuma Principe.

An zaɓe shi gwamnan Adamawa a 1998. Daidai lokacin da yake a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan, sai zaɓaɓɓen Shugaban Qasa ya zaɓe shi don ya mara masa baya a matsayin mataimakinsa.

Yunƙurinsa na maye gurbin Obasanjo a ƙarshen wa’adin mulkinsa ya ci tura bayan da ya yi ta yin takun-saka tsakaninsa da Obasanjo, sannan ya fuskanci ƙalubalen shari’a, har ta kai ga daga bisani suka kare a Kotun Ƙoli ta Nijeriya, wadda ta bai wa Hukumar Zaɓe (INEC) umarnin sanya sunan Atiku a jerin ‘yan takara.

Ya yi takarar shugaban kasa ta farko ƙarƙashin tutar jam’iyyar AC, bayan da ya fice daga jam’iyyar PDP, al’amarin da ya haifar masa koma-baya a zaɓen 2007, inda ya zo na uku, bayan Umaru Yar’Adua na jam’iyyar PDP da Muhammadu Buhari na Jam’iyyar ANPP.

Atiku Abubakar ya fafata da Shugaban Ƙasa mai ci, Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC mai mulki a ranar 16 ga Fabrairun 2019, zaɓen da bai yi nasara ba.

Nyesom Wike
An haife shi a ranar 13 ga watan Disambar 1963, a garin Rumuepirikom da ke Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor ta jihar Ribas.

Tun da farko ya fara aikin lauya ne bayan da ya halarci Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas kafin daga baya ya shiga siyasa, kuma a halin yanzu shi ne gwamanan Jihar Ribas na shida cikin jerin gwamnonin jihar da aka yi kawo yanzu.

Ɗan jam’iyyar adawa ta PDP ne.
Gwamnan na Ribas ya fara shiga siyasa ne bayan da aka zaɓe shi a matsayin shugaban Ƙaramar Hukumar Obio Akpor ta jihar ta Ribas a shekarar 1999, muqamin da ya riƙe har zuwa 2007, bayan da aka sake zaɓensa ga muƙamin a 2003.

A 2007, gwamnan jihar a wancan zamanin Rotimi Amaechi ya naɗa shi shugaban ma’aikata a fadar gwamnan jihar da ke birnin Fatakwal. A watan Yulin 2011, tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya naɗa shi ƙaramin minista a ma’aikatar ilimi ta ƙasar, kuma daga baya ya samu ci gaba zuwa babban ministan ilimi a shekarar 2013.

Sai dai daga baya ya ajiye muƙamin domin tsayawa takarar gwamnan jihar Ribas a zaɓen gwmnanoni 2015. Bayan ya shafe shekara huɗu na wa’adinsa na farko na gwamnan jihar, Wike ya sake tsayawa takarar muƙamin kuma ya lashe zaɓen, kuma an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Yanzu yana cikin Waɗanda suka ayyana ƙudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Peter Obi
Peter Obi tsohon gwamnan Jihar Anambara ne daga 2006 zuwa 2013, kuma ya bayyana cewa yana son zama shugaban Nijeriya a zaɓen shekara mai zuwa ta 2023.

An haife shi ne a ranar 16 ga watan Yulin 1961, kuma ya kasance ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa ne, inda ya taɓa zama ɗan takarar mataimakin shugaban Nijeriya a jami’iyar adawa ta PDP a zaɓen 2019.

Ya halarci Kwalejin Christ the King College a Onitsha, da Jami’ar University of Nigeria ta Nsukka da kuma Harvard Business School, da ke birnin Boston na Amurka.

Sau biyu yana tsayawa takarar muƙamin gwamnan jiharsa ta Anambara a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a 2003, amma yana faɗi a zaɓukan, sai dai bai karaya ba, inda ya nufi kotunan ƙasar kuma suka tabbatar masa da nasara.

Ya fuskanci tuhume-tuhume kan rawar da ya taka bayan wata badaƙala mai suna Pandora Papers ta bayyana, wadda wasu ‘yan jarida suka bankaɗo yadda wasu jami’ai da shugabannin gwamnatocin ƙasashen duniya ke sace kuɗaɗen al’umominsu kuma suke voye su a ƙasashen ƙetare.

Sunan Peter Obi ya bayyana a cikin qasidun da aka bankaɗo, amma ya sha musanta cewa ya karya dokokin Nijeriya kan batun. Sai dai shugaban Nijeriya ya umarci hukumomin tsaron ƙasar, musamman ma hukumar EFCC da su binciki dukkan Waɗanda sunayensu suka bayyana cikin rahoton na Pandora Papers.

Yanzu yana cikin Waɗanda suka ayyana ƙudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Aminu Waziri Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal shi ne Gwamnan Jihar Sakkwato kuma halastaccen ɗan jam’iyyar adawa ta PDP da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar muƙamin shugaban ƙasa a shekara mai zuwa.

Tsohon ɗan majalisar wakilan Nijeriya ne, har ya taɓa riqe shugaba majalisar a watan Yunin 2011 zuwa watan Yunin 2015.

An haifi Aminu Waziri ranar 10 ga watan Janairun 1966 a ƙauyen Tambuwal da ke jihar Sakkwato. Ya shiga makarantar firamare a 1979 sannan ya shiga kwalejin horas da malamai ta Dogon-Daji a 1984.

Daga nan kuma ya shiga Jami’ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, inda ya karanci aikin shari’a a 1991. Tambuwal ya fara koyon harkokin majalisa daga 1999 zuwa 2000 lokacin da yake aiki a matsayin mataimaki kan harkokin majalisa ga Sanata Abdullahi Wali, wanda a lokacin yake riqe da muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa. A 2003, ya nemi kujerar wakiltar mazaɓar Kebbe da Tambuwal a Sakkwato.

An zave shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam’iyyar ANPP. ‘Yan watanni gabanin zaɓen gwamna a 2007, Tambuwal ya koma PDP tare da tsohon gwamnan Sakkwato. Tambuwal ya riƙe muqamai a majalisar wakilai. A 2005, ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai har zuwa lokacin da ya koma PDP.

Bayan an sake zaɓarsa a 2007, an kuma sake zaɓarsa a matsayin mataimakin shugaban bulaliyar majalisar. Tambuwal ya kuma riƙe shugabancin kwamitocin majalisar da dama ciki har da kwamitin dokoki da kasuwanci da na sadarwa da kuma na shari’a.

Ya kuma kasance mamba a kwamitin wucin gadi kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasa garambawul. A watan Yunin 2011 ne Aminu Waziri Tambuwal ya zama shugaban majalisar wakilan Nijeriya ta 10 a cikin wani yanayi mai sarƙaƙiya kuma na ba-saban-ba.

Bala Muhammad
An haifi Bala Muhammad a ranar 5 ga watan Octoban 1958, a Ƙaramar Hukumar Alƙaleri da ke Jihar Bauchi a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Ya fara karatunsa na firamare a shekarar 1965 a wata makaranta da ke ƙauyen Duguri, inda ya kammala a shekarar 1971. Daga nan ya tafi makarantar sakandire a shekarar 1972, inda ya kammala a shekarar 1976.

Ya halarci Kwalejin Kimiyyar Zane-Zane ta Shiyyar Arewa Maso Gabashin Nijeriya daga shekarar 1977 zuwa 1979. Daga nan kuma sai ya soma karatunsa na digirin farko a Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno a shekarar 1979, ya kuma kare a 1982, inda ya karanci harshen Ingilishi. Bala Muhammad, ya kuma halarci Kwalejin Horas da Harkokin Gudanarwa a inda ya samu horo na ɗan wani lokaci.

Ƙauran Bauchi tsohon ɗan jarida ne, an shafe tsawon shekaru ana gungurawa da shi a harkar. Tsohon edita ne da rusasshiyar jaridar ‘The Mirage’ a shekarar 1982 -1983, sannan tsohon mai aika rahotanni ne ga Kamfanin Dillacin Labaran Nijeriya (NAN).

Ya yi aiki da tsohuwar jaridar The Democrat, 1983 zuwa 1984, sannan ya yi aiki da ma’aikatar cikin gida ta Nijeriya tsakanin shekarun 1984 -1994.

Ƙauran Bauchi ya taɓa zama babban jami’in shigo da kayayyaki a ma’aikatar albarkatun qasa ta Nijeriya tsakanin 1995 -1997, kazalika ya taɓa zama mataimakin darakta a ma’aikatar wuta ta Nijeriya tsakanin 1997 -1999.

A shekarar 2003 ne ya zama daraktan gudanarwa na hukumar sufurin jiragen ruwa ta Nijeriya. Daga bisani ne kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati a ƙashin kansa ya kuma tsunduma siyasa.

A shekarar 2007 ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP a matsayin ɗan majlisar dattawa mai wakiltar Bauchi ta Kudu har ma ya yi nasara daga shekarar 2007 zuwa 2010. Sanata Bala Muhammad ya riƙe muƙamin ministan Abuja daga shekarar 2012 zuwa 2015.

An ruwaito cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da Shugaba Jonathan. A lokacin zaɓukan 2019 ne Bala Muhammad ya tsaya takarar gwamnan Bauchi ƙarƙashin jam’iyyar PDP kuma hukumar zaɓen Nijeriya wato INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaven. Wannan lamari ya sa EFCC ta dakatar da binciken da take masa saboda kariya da yake da ita a matsayinsa na gwamna kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Bayan zuwa kotuna har uku kan ƙalubalantar sakamakon zaɓen da abokin takararsa Mohammed Abubakar ya yi a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe da Kotun Daukaka Ƙara, a ƙarshe Kotun Ƙoli ta tabbatar wa da Bala nasararsa. Yanzu yana cikin Waɗanda suka ayyana ƙudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.

Abubakar Bukola Saraki
An haifi Sanata Abubakar Bukola Saraki ne ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 1962 a garin Ilorin na Jihar Kwara.

Sanata Bukola ɗa ne ga Alhaji Abubakar Olusola Saraki, fitaccen ɗan siyasar ƙasar, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa. Ya yi karatunsa a King’s College, Legas daga 1973 zuwa 1978, da kuma kwalejin Cheltenham a London, tsakanin 1979 zuwa 1981. Haka kuma ya yi digirinsa na farko a fannin likitanci a Kwalejin kiwon lafiya ta asibitin Landon tsakanin 1982 zuwa 1987.

Ya shiga harkokin siyasar Nijeriya a shekarar 2000, kuma ya yi takarar gwamna, inda aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Jihar Kwara a shekarar 2003, sannan aka sake zaɓen sa a shekarar 2007.

Sanata Saraki, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan Jihar Kwara, ya daɗe yana fuskantar zargin cin hanci da kuma halatta kuɗin haramun.

A baya ya fuskanci shari’a bisa zargin qin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Ƙolin Nijeriya ta wanke shi a shekara ta 2018. Haka kuma Sanata Saraki ya zama ɗan majalisar dattawan Nijeriya a shekarar 2011, kuma an sake zaɓen sa a shekarar 2015.

An zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa babu hamayya a ranar 9 ga watan Yunin 2015. Yanzu yana cikin Waɗanda suka ayyana ƙudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.

Anyim Pius Anyim
Shi ma tsohon kakakin majalisar dattawan Nijeriya Anyim Pius Anyim ya bayyana sha’awarsa ta zama shugaban Nijeriya a shekarar 2023.

An haife shi ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 1961 a Ƙaramar Hukumar Ivo ta jihar Ebonyi, kuma ya halarci makarantar Ishiagu High School, inda daga baya ya je jami’ar jihar Imo da ke Uturu daga 1983 zuwa 1987.

Ya shiga siyasa a shekarar 1998 bayan da ya shiga jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) kuma aka zaɓe shi ga muƙamin sanata. Sai dai bayan mutuwar tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya Janar Sani Abacha, a wata Yunin 1998, an soke zaɓen.

Amma daga baya ya shiga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), a zamanin shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar, inda ya sake tsayawa takara kuma aka zaɓe shi muƙamin sanata a 1999.

Ya zama shugaban majalisar dattawa a watan Agustan 2000 zuwa Mayun 2003, bayan da aka sauke Marigayi Chuba Okadigbo daga muƙamin. Ya tava riqe muƙamin Sakataren Gwamnati Tarayyar Nijeriya daga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2015. Yanzu yana cikin Waɗanda suka ayyana ƙudirinsu na takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa ta PDP a zaɓen 2023.

Dele Momodu
An haife shi ne a watan Mayun shekarar 1960, kuma ɗan jarida ne mai zaman kansa mai wallafa wata mujalla mai suna Ovation International, baya ga zama ɗan kasuwa.

Ya halarci jami’ar Ife, wadda aka sauya wa suna zuwa Jami’ar Obafemi Awolowo, da ke garin Ile-Ife a 1982. Ya riƙe muƙamin sakataren tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo Chief Akin Omoboriowo tsakanin 1983 zuwa 1985, kuma daga 1986 Momodu ya koma fadar basarake na Ife – wato Ooni of Ife, Oba Okunade Sijuwade Olubuse II.

Bayan ya bar aiki da Ooni na Ife, sai Jami’ar Professional Studies, Accra, Ghana, ta ba shi digirin yabo ta Doctor of Humane Letters. Ya shiga gwagwarmayar siyasa, inda a 1993, Momodu ya shiga ƙungiyar siyasa ta Moshood Abiola mai neman shugabancin Nijeriya a wancan zamanin.

An kama shi daga baya kuma aka tsare shi a wani ofishin ‘yan sanda a Legas, inda ya ce ‘yan sanda sun azabtar da shi. Gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ƙarƙashin Janar Sani Abacha ta sake kama shi a 1995 kuma ta tuhume shi da aikata laifukan cin amanar ƙasa, kuma cikin laifukan da aka tuhume shi da aikatawa akwai na kafa wani gidan rediyo mai suna Radio Freedom wanda aka sauya wa suna zuwa Rediyo Kudirat (matar marigayi MKO Abiola) daga bisani – bayan da aka kashe ta.

Ya tsere daga Nijeriya zuwa Birtaniya inda ya shafe shekaru uku yana zaman gudun hijira. Yana daga cikin ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP da suka bayyana aniyar neman kujerar shugabancin Nijeriya a 2023.

‘Yan takarar wasu jam’iyyun:

Rabiu Musa Kwankwaso
An haifi Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Lahadi 21 ga Oktoba na 1956, a ƙauyen Kwankwaso da ke a Ƙaramar Hukumar Madobi ta Jihar Kano.

Rabiu Musa ya halarci makarantar ƙere-ƙere da ke a garin Wudil da kuma Kwalejin Fasaha ta Kano, bayan nan ya karasa makarantar Kaduna Polytechnic da ke Jihar Kaduna.

Fitaccen ɗan siyasa ne, inda ya riƙe matsayin gwamna a Jihar Kano har sau biyu, wato a shekara (1999 zuwa 2003), da kuma shekara ta (2011 zuwa 2015).

Shi ne kuma gwamnan farko na Jihar Kano a Jamhuriya ta Huɗu kuma ya ci zaɓe ne duk a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kafin daga bisani ya sauya sheƙa ya koma jam’iyyar APC.

A zaɓen shekara ta 2003, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rashin nasara ne a hannun Malam Ibrahim Shekarau. A watan Yuli a shekara ta 2003, Olusegun Obasanjo ya naɗa shi a matsayin Ministan Tsaron Nijeriya.

A shekara ta 2015, Kwankwaso ya yi rashin nasara a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaven fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, daga bisani sai ya sake sauya sheƙa zuwa takarar kujerar Sanata wanda a nan ne ya samu nasarar cin zaɓen.

A shekara ta 2018, ya fice daga jam’iyyar ta APC inda ya sake komawa jam’iyyar PDP da niyyar yin takarar Shugaban Ƙasa, sai dai ya sha kaye a hannun abokin karawarsa Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani wanda aka gudanar a garin Fatakwal.

Kwankwaso ya riƙe muƙamai da yawa a Jihar Kano dama qasar Nijeriya baki ɗaya, waɗanda suka haxa da aikin gwamnati da na siyasa. Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a watan Janairu a shekara ta 1992 zuwa watan Nuwamba a shekara ta 1993.

Babban Jakadan Nijeriya a Dafur a shekara ta 2007 zuwa shekara ta 201. Sanatan Kano ta Tsakiya, 11 ga watan Yuni a shekara ta 2015 zuwa shekara ta 2019. Yanzu ya yanki takardar neman takarar shugaban ƙasa a sabuwar jam’iyyar da ya koma ta NNPP bayan ficewarsa jam’iyyar PDP.

Kingsley Moghalu
Kingsley Chiedu Moghalu sanannen ma’aikacin banki ne wanda ya tava tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaven 2019. An haife shi ne a jihar Legas a 1963 kuma ya girma ne a ƙasasshen Switzerland da Amurka inda mahaifinsa ya yi aiki.

Masanin tattalin arziki ne, inda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwamnan Babban Bankin Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua daga 2009 zuwa 2014. Ya kafa wani kamfani mai zaman kansa mai suna Sogato Strategies LLC a birnin Geneva, kamfanin da ke bayar da shawara kan yadda ake zuba jari a kamfanoni. bayan da ya bar aikin da ya yi a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Daga baya ya koyar a Jami’ar Tufts daga 2015 zuwa 2017. A halin yanzu shi ne ɗan takarar muƙamin shugaban ƙasa a jam’iyyar Young Progressives Party (YPP), takarar da ya daɗe yana yi tun zaɓen 2019.

Khadijah Okunnu-Lamidi
Khadijah Okunnu-Lamidi ita ce mace ta farko da ta fito fili ta bayyana sha’awar tsayawa takarar shugabar ƙasa a zaɓen 2023. Shekarun Khadijah 38 da haihuwa, kuma an haife ta ne a Jihar Legas, kuma mahaifinta shi ne Lateef Olufemi Okunnu, tsohon Ministan Ayyuka a tsohuwar gwamnatin farar hula.

A ɓangaren ilimi, Khadijah ta halarci Jami’ar Boston da Jami’ar Heriot-Watt waɗanda dukkansu ke da rassa a Dubai, inda ta sami digiri na ɗaya da na biyu. Khadijah Okunnu-Lamidi ta kafa wani kamfani mai suna Slice Media Services mai harkar yaɗa labarai da tallace-tallace a Nijeriya.

Adeshola Lamidi, wani ƙwararre ne kan harkar kasuwancin zamani da zuba jari ne mai gidanta kuma suna da ‘ya’ya tsakaninsu. A cikin Afrilun 2022 ta shiga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), wadda ta ce ra’ayinta ya yi daidai da manufofin jam’iyyar.

Dr. Nicolas Felix
Dr. Nicolas Felix ɗan siyasa ne mai shekara 41 da haihuwa, kuma an haife shi ne a birnin Auchi na Jihar Edo. Shi ne shugaban kamfanin Miracle Center International, da Zoe Homecare Agency da Victory Security Company da wasu kamfanonin.

Ya halarci makarantar tarayya ta Federal Polytechnic, Auchi jihar Edo, kuma yana da digiri na biyu da na uku daga Jami’ar Ames Christian University a birnin Florida na Amurka, da kuma Jami’ar CICA International University & Seminary a jihar New York ta Amurka.

Dr. Nicolas Felix shi ne ɗan takarar jam’iyyar siyasa ta Peoples Coalition Party of Nigeria PCP kuma yana cikin matasa masu ƙarancin shekaru da ke fafutukar ganin tafarkin dimukraɗiyya ya wanzu a Nijeriya. Mazaunin birnin New York ne na Amurka, kuma ya ce yana da yaƙinin warware matsalar ƙarancin hasken lantarki da ta addabi Nijeriya.

Mojisola Adekunle-Obasanjo
A haifi Mojisola Adekunle-Obasanjo a ranar 10 ga watan Agustan 1944, kuma mace ce da ta yi aikin soja har ta kai ga muqamin Manjo a rundunar sojin Nijeriya. Ita ce ta kafa jam’iyyar Masses Movement of Nigeria a 1998 kuma ta tsaya takarar muqamin shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar wannan jam’iyya ta MMM a 2003.

Ita ce kuma mace ɗaya tilo da ta tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2007 a Nijeriya. Mojisola Adekunle-Obasanjo tsouwar matar shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ce. Ta tava yin aiki a matsayin ma’aikaciyar lafiya a rundunar sojin Nijeriya kafin daga baya ta amince ta tsaya takara a 2003. A bana ma ta bayyana aniyarta ta yin takara ƙarƙashin jam’iyyarta ta Masses Movement of Nijeriya.

Chukwuka Monye
An haife shi a watan Yulin 1979, kuma yana alfahari cewa shi ɗan Nijeriya ne, wada duk da cewa ya sami damar komawa wata ƙasar da sauya ƙasarsa ta asali, har zuwa wannan lokacin fasfon Nijeriya ne kawai yake riƙe da shi.

Ya halarci makarantar sakandarensa ne tare da ɗalibai daga wasu jihohin Nijeriya, inda ya ƙulla alaqa da yawancinsu. Ya fara halartar Jami’ar jihar Ogun kafin daga baya ya koma Amurka, inda ya halarci Jami’ar Warner University. Yana kuma da digiri na biyu daga Jami’ar Oxford. Yana fatan zama shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar African Democratic Congress. Mazaunin birnin Asaba na jihar Delta ne.

Tunde Bakare
Tunde Bakare ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Muhammadu Buhari a shekarar 2011.
Sai dai bayan wannan lokacin, Fasto Tunde Bakare, ya ce gwamnatin shugaban ƙasar ta jefa Nijeriya a halin koma-baya maimakon ci gaba.

Tunde Bakare fasto ne a cocin The Citadel Global Community Church (CGCC) a Nijeriya. Ya ce tun da farko an haife shi Musulmi ne amma daga baya ya shiga addinin Kirista a 1974.

Bakare ya halarci Jami’ar Legas tsakanin 1977 zuwa 1980, kuma ya zama lauya bayan da ya halarci Makarantar Lauyoyi a 1981, inda ya fara aiki da shahararren lauyan nan Gani Fawehinmi da Rotimi Williams & Co da kuma Burke & Co, Solicitors.

Daga baya ya buɗe na shi ofishin mai suna Tunde Bakare & Co (El-Shaddai Chambers) a watan Oktoban 1984. A watan Mayun 1988 ya sauya sheƙa, inda ya bar aikin lauya kuma ya kafa cocin nasa.

Tun bayan raba gari da suka yi da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Tunde Bakare ya ci gaba da haxa siyasa da aikinsa na fasto, kuma yana cikin ‘yan Nijeriya da ake sa ran za su taka rawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sai dai zuwa yanzu bai bayyana sunan jam’iyyar siyasar da zai tsaya takara a ƙarƙashinta ba.