Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga PORTIA ROELOFS

Cigaba daga makon jiya.

A waɗannan lokutan da tafiyar gobe-yau-jiya ke gudana, wato Time Travel ga tunanin Farfesan, a lokaci guda kuma jasadinsa da ruhinsa suka kasa mayyaze da bambance shin har yanzu a cikin Saharar Maiduguri suke ko kuma a katafaren gurin da ake kira da Queens College Oxford da ya ke a Jamiar Oxford suke. Sai ya cigaba da sambatun sa kamar haka: Maimakon na bi ta ƙofofin zinare da azurfah na Aljannah, kullum abunda na fi so sama da hakan shi ne na roƙi alfarmar St Paul ko zan iya zama kusa da shi na ɗan wani lokaci ko na samu tabarrakinsa yayin da burujin Duniyar da nake ciki ke cigaba da jujjuyawa…. Sai da yayi gyaran murya sau biyu kafin ya ajiye ƙarshen maganar tasa da cewa, Daga nan kuma sai na zuba wa sarautar Allah ido na ga mai zai faru da ni. 

Sai kuma ya ƙara cigaba da saƙa zaren labarin nasa na farko kamar haka: ko kuma, sai ya ɗago kansa ya kalle ni da giransa a tashe da ƙwayoyin idanuwansa masu haske da kana kalla, ka san rashin lafiya ta ziyarce su, ya ɗora da faɗin, Ko kuma kai tsaye na zarce ga Ubangiji na roƙe shi ko zan iya samun a yi min Duniya ta ni kaɗai, wato ‘Planet’. Zan nemi hakan ne saboda na samu damar yin bincike-bincike da gwaje-gwaje na kimiyya. 

Bayan shafe shekara guda cur yana jinya a asibitin St Luke na birnin Oxford, sai ya tayar da borin sai an dawo da shi Najeriya. Hakan ya faru ne sanadiyyar ƙawazuci da bege da ya cika shi na dawowa ƙasar domin ya kammala ayyukansa da sauran bincike-bincikensa. Wato projects-projects ɗinsa da bai qarasa ba. A lokacin ofishin hulɗar jakadancin Birtaniya da ƙasashen waje, wato Foreign Office yana gargaɗin duka mazauna Birtaniyar a kan guje wa tafiya zuwa jihar Borno saboda haɗarin hakan. Amma hakan bai tanqwara niyyar Farfesan ba na fasa dawowa jihar Maidugurin. 

Lokacin da ya sauka a garin a watan Nuwambar shekarar 2016 a keken tura marasa lafiya aka kawo shi, saboda raunin da jikin nasa ya yi. Komai mai yiwuwa ne a wajen Farfesa, bai san wata kalma wai ita mara yiwuwa ba a ƙamus ɗinsa. Haka Maryam, wato tsohuwar ɗalibansa ta furta yayin da zuciyarta take cike da alhini, muryarta cikin raurawa da tausayi. A daren da ya sauka a Maidugurin, Sule ya kira ni, yana shaida min cewa Farfesa ya galabaita, amma duk da hakan, bakinsa har yanzu yana jin daxin ɗanɗano abincin da yafi so, wato farfesun hantar kaza. 

Himma ba ta ga rago! Da wayewar gari, sai Farfesan da mai kula da shi, wato Sule suka fara sababbin shirye-shirye na yadda za su kammala gagarumin aikinsu na dasa bishiyoyin gida a faɗin yankin Maidugurin. Sunan project ɗin nasu, Indigenous Trees Project.

Tabbacen abu ne, cewa dukkanin rubututtukan taaziya na ƙarewa ne da abu iri ɗaya, wato:  Farfesa Richard ya riga mu gidan gaskiya a yau 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2016 a jihar Maiduguri. Ya rasun ne gajeriyar jinya da ya yi. Ya mutu ya bar ɗan uwansa da ake kira da Martian, da kuma yarsa Anita. 

Duk da yawan tattaunawar da na yi da shi da kuma ]imbin bayanan da ya ba ni game da shi da rayuwar sa, har yanzu lankafaffun takardun da na ware na ɗaukar shiftar bayanansa da kuma shekararsa ta ƙarshe a Oxford har yanzu takardun ban cika su ba. Lokacin da na tsara zan ware watan Janairu domin rubuta marsiyyar Farfesan, wato taaziyyarsa, na yi tunanin nan da nan zan yi na gama. Ina ganin tunda Farfesan ya riga mu gidan gaskiya kuma ba na ganin sa da idanuwana na zahiri kamar zan fi samun damar sanin haƙiƙarsa da kuma ayyukan da ya yi a rayuwarsa.

A wannan bazarar ne tafiya ta ƙara kama ni zuwa Maidugurin domin bincike mai alaƙa da karatuna. Shekaru takwas kenan da zuwana jihar Maidugurin; wanda ya zo daidai da watanni shida da rasuwar Farfesa. Har yanzu surar hotonsa babba na kafe a bangon falonsa a ƙasan wannan kujerar tasa da yake ji da ita. An gudanar da janaizar tasa ne a tsakiyar muku-mukun sanyi, lokacin da busasshiyar Iskar Sahara ke kaƙawa da busawa tsakankanin masu gudanar da janaizar tasa wacce ta samu halartar mutane ɗaruruwa.

Yaba kyauta, tukuici. Inji Mallam Bahaushe. Gudunmowar da Farfesan ya bayar ne ya sanya Jamiar Maidugurin da ya koyar na tsawon shekaru suka sadaukar da dashen bishiyoyin da ya assasa gare shi ta hanyar bayar da isasshen filin da za a daddasa su. Hakan ce ta sanya Sulen ya gusa daga gidan Farfesan da yake zaune da iyalansa zuwa ƙarshen katangar Jamiar.  Ya yi hakan ne domin samun sauƙi wajen kulawa da bishiyoyin da suka dasa guda dubu ashirin (20,000) kafin Farfesan ya riga mu gidan gaskiya. 

Amma waɗannan abubuwan na sama kamar inuwarsa ne, ko kuma sadaƙatul jariyah da ya bari a Duniya. Watarana, Ina cikin duba sunayen dake kan Wasaf ɗi na, sai na ga ashe sunan Farfesan na daga sunayen da nake Wasaf da su. Wani hotonsa ne a kan shafin nasa yana kallon sararin samaniya a lokacin da saman ta yi shuɗiya kamar wacce aka zana; gwanin shaawa. 

Na tuttura wa mutanensa da hotunansa a lokacin da ya yi wata tafiya a ƙaramin jirgin ruwa a Dam ɗin da ake kira da Alam da yake a Tafkin Chadi a shekarar 2009. Wannan hoton ne babbar yar Sule da ake kira da Zainab ta saka a matsayin hoton shafin  Wasaf ɗin ta. 

Da na ga babu wani ƙwaƙƙwaran dalili da zai sa na cigaba da zama a Maidugurin, sai zakara ya ba ni saa na hau jirgi, sai Birnin Sarauniya, wanda mu a can muke wa kirari da Queens. Daga baya ne ya bayyana gare ni cewa, akwai bayanan Farfesan a kundin adana bayanan tsofaffin ɗalibai na Jamiar ta Oxford ɗin da ake kira da College archive. Hakan ya faru ne wata rana bayan na yi wa sakatariyar kula da sashin adana bayanan tsofaffin ɗaliban mai suna Jen. Kayan nama ba ya kashe kura.

A wannan rumbun, na san zan iya yin tsintuwar zarurrukan da zan ƙwarara saƙar da na yi ta rayuwar Farfesan da zarurrukan da na san kaurinsu da  ƙwarinsu ba su kai wanda zan ci karo da su a rumbun ba. Tsahon ran rayukan labarurrukan da ya labarta min na rayuwarsa da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar tasa ya kai wajen shekaru 900 Idan ka ja gezarsu ka kuma tufke su a marin da ka fara saƙar tasu daga nan. Jirgin ƙasa na hau mai zuwa Oxford.

Na haɗu da sakatariya Jen ne a wani ofishi mai rufin sili dogo kamar zanƙalaƙoƙi dake da kusurwa huɗu dake kallon lambun da ake kira da Provost Garden, wato shugaban kwaleji dake ƙarƙashin Jamiar Oxford. Idan ka ƙura wa bishiyoyin dake cikin lambun na-mujiya, ka kuma wurga maganan naka dai har ila yau ga gilasan dake maƙwabtaka da bishiyoyin, sai ka yi tunanin kamar auren zobe ne tsakanin bishiyoyin da suka baibaye lambun da kuma gilasan da suke kallon sa waɗanda sun kai shekaru 100 da wannan aure! Da muka shiga, sai Jen ta miqo min kundin adana bayanan ɗaliban shekarar 1940. Ga hotonsa sanye da irin rigar nan jacket da ake fi saqa ta a ƙasar Scotland.

Duk da hotonsa nasa baƙi da fari ne; hakan bai hana bayyana kalar shuɗayen ƙwayoyin idanuwansa ba da Turawa ke wa laƙabi da ‘pale blue eyes’. Wani ɗan gajeren bayani a kansa ya bayyana addininsa da wani addini mai suna CofE. Haka kuma shi ne ya lashe lambar yabo daraja ta ɗaya a gasar baje kolin fasaha da aka yi mai suna Riggie Exhibition lokacin yana aji biyu a Jamiar.  Har ila yau, ya fita da sakamako mai daraja ta farko, wato first class a lokacin da ya gama digirin sa na farko a ɓangaren kimiyyar rayuwar dabbobi da ake kira da ‘Zoology’ a shekarar 1942. A cikin shekara uku kacal, ya kammala digirinsa na uku, lokacin ba a fi wata uku da ayyana samun zaman lafiya a Nahiyar Turai ba. A cikin kundin adana bayanan ɗalibai a ƙasan gurin da aka rubuta Academic Distinctions, College Offices, Sports and Athletics babu komai. Wajen da ake rubuta sanaar ɗalibi shi ma ba a zayyana komai a wajen ba. 

Saboda karamci, sai ta nemi da ta yi min kwafe na shafin dake ɗauke da bayanan Farfesan, ta kuma ba ni shawarar da na tuntuɓi iyalan Farfesan domin samun ƙarin bayanai a kansa, ko kuma na tuntuɓi wacce ta gada, wacce yanzu ita ce jami’ar sadarwa ta kwalejin. Ta taimaka wajen buga tarihin rayuwar Farfesan da ya rubuta da kansa da ya kira da Queens at War a mujallar  kwalejin da kwalejin take wallafawa da a shekarar 2010 bayan dawowa ta daga Maidugurin (alal haƙiƙa wannan rubutun da aka buga a College Magazine su ne Waɗanda na rubuta daga shiftar da ya yi min ina rubutawa, kuma su ne wasu daga shafukan da ba a samu damar tattara su ba da yar wajensa Anita ta turo min bayan rasuwarsa.)

Sai na ga hanya ta vace min a dogon kwararon da muka biyo da kuma wasu hanyoyin da a da na bi su na tsohuwar kwalejin tawa. Da na ƙwanƙwasa farar ƙofar ofishin Mista Emily, sai ƙwaƙwalwata ta harbo min hotonta da duk lokacin da na zo karanta Mujallar Kwalejin nake yin tozali da ita Idan na kalli shafin bangon jaridar na baya. Sai na gan ta jin ta ya fi ganin ta. Kodayake dai yadda take tsaga dogon gashin kanta ya kwanta gwanin sha’awa, dole ya ba wa mai kallo sha’awa. Sai na same ta har yanzu wushiryarta na nan ɗaras a tsakankanin fararen haƙoranta reras da su. 

Mutuwa rigar kowa! Shi ne Uba a duk lokacin da za a yi wani taro a kwalejin nan, ya girmi kowa…. ta furta cikin alhini, muryarta sanyaye.

Yadda take bayani a kan Farfesan za ka iya cewa ba wani tuna shi sosai da sosai ta yi ba, yadda ya kamata. Haka nan idan ka nutsu sosai sai ka ga kamar Inuwarsa ta gani kawai ba gangar jikinsa ba. A lokacin da nake fitowa daga ɗan ƙaramin ofishihnta wanda wata bishiya mai faka-fakan fararen fure masu danƙo idan ka kai hannu gare su, da ake wa laƙabi da magnolia tree. Na ɗaraso zuwa inda na haɗu da sakatariya Jen. Sai na ji kamar ba ta biya ni ba. Ba ta biya ni ba mana! Kamata ya yi a ce a matsayinta na tsohuwar mai adana bayanan tsofaffin ɗaliban kwalejin dake ƙarƙashin kulawar Jamiar Oxford ta tuna tare da baje min zare da abawa a kan Shehin Malamin, amma sai ya zamanto ga abawar a hannunta riƙe, amma ta kasa lalubo zaren da za ta saƙa min saƙar rayuwar wannan bawan Allah da ya bar mahaifarsa ya shiga Sahara domin canza rayuwar wasu mutanen da Annabi Adamu ne kaɗai ya haɗa su a nasaba. Ba dangin iya ba ko na Baba! Na samu wasu qarin bayanai a kan Farfesan a wajen shugaban  Kwalejin, duk dai shi ma ba wasu bayanai ba ne da za a yi ta-kanas-ta Kano domin zuwa safararsu ba, amma dai sun taimaka. Amma duk da waɗannan ƙarin bayanan da na samu daga shugaban kwalejin, hakan bai ƙara min haske ga sanin da na yi wa shi Shehin Malamin ba. Farfesan Farfesosi. Zaki ba ka fargaba. Gwanki sa gabanka inda ka ke so. Fari mai farar aniya. Farin Bature na farar Sarauniya! 

A wannan ranar a Oxford ne na kunce dukkanin saƙar zarurrukan labaran da Farfesa ya ba ni a kansa dangane da rayuwarsa, haka kuma na dinga bi ina feɗe darussan dake cikin rayuwar tasa har wutsiya: tun daga ranar da wayar salula ta ta yi rauji yayin da ya kira ni ta wayar tawa Ina saman ɗakin benen gidanmu, zuwa yadda muka dinga haɗuwa da shi a Farmers Club, sannan na gangaro yadda muka shafe wata guda cur ni da shi a Maiduguri a gidansa yayin da taurari suka ƙawata sararin samaniya yana saƙa min zarurrukan labaran gwagwarmayarsa ni kuma Ina tufkewa.

Ba wai tsuran labarurrukan rayuwar tasa ba ne abunda na hakaito daga shi ɗin ne babban darusan da na koya ba, a’a, zaman da na yi da shi ne da abubuwan da na gani ne da idanuwana a ƙarshe-ƙarshen rayuwar tasa ne abubuwan da suka fi tava ni. Zuciya takan iya manta sautukan da ta ji ta fatun kunnuwa, amma da wahala ta sha’afa ga abubuwan da suka faru da ita na kyautatawa ko akasin hakan. Daga cikin irin waɗannan waƙi’an, abubuwan da suka faru sun haɗar da gudunmowarsa da ya aiko lokacin bikin Miss Emily ta wani ƙayataccen zanin gadon da aka yi da kaɗaɗɗiyar farar tausasassar audugar ƙasar Masar tun daga Maiduguri har Birnin Oxford. Haka nan da yadda yana kan gado a asibiti a Headington ya ringa shiftar wasiqa ga babbar jaridar nan ta ƙasar Ingila da ake kira da Guardian mai taken a home of rest for dictators, wanda a cikinta ne ya bayyana min yaya ma sunan jirgin ruwan da Napoleon ya yi amfani da shi a qarni na 18 yayin mamayar Nahiyar Turai. Kai har ma da yadda ya tattaka matattakalar bene mai hawa 90 yayin shiga kallon wani babban fim a kan kimiyyar almara da ake kira da sci-fi film Silimar da ake kira da Marble Arch Odeon da muka je tare shekaru biyu da suka wuce. Kai! fim ɗin ya ja ni sosai, ya faɗa yayin da aka fara taken lamba, kawai dai duk lokacin da suka samu savani, sai su kaure da faɗa. 

Kullum Ina kwatanta sanin da na yi wa Farfesa tamkar labarin makafin nan ne guda huɗu da kowannen su ya siffanta giwa da iya kaɗai sashin jikinta da ya taɓa. Duk ƙoƙarin da na yi don na zayyana rayuwarsa a haƙiƙar yadda take a cikin waɗannan shafukan da ke tsakankanin  tafukan hannayenka, hakan ya ci tura. Ta yaya ma hakan za ta kasance? Sanin bawa zahiri da baɗininsa dama ai sai Mahaliccinsa. Rubutuna a kan wannan Shehin Malami a Boko tamkar wanda ya ƙura wa kogi idanu ne yake so ya kama kifaye, zai kama abunda ya kama ne ya gaji ya tafi ba tare da ya kame kifayen kogin duka ba. Amma ni har yanzu Ina gaban kogin ko zan iya cika burgamin nawa kuwa ko kuwa a’a.
Ƙarshe!

Wanda ya fassara ƙasidar shi ne, Mudassir S. Abdullahi, ɗalibi a Jamiar Bayero da ke Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *