Gwamnatin tarayya ta sake buɗe iyakokin ƙasa a wasu jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Juma’a ne gwamnatin tarayya ta amince da sake buɗe wasu ƙarin kan iyakokin ƙasar guda huɗu da aka rufe a watan Agustan 2019 a wani mataki na daƙile fasa ƙwauri da bunƙasa noman shinkafa a cikin gida a ƙasar nan.

A wata sanarwar da hukumar kwastam ta Nijeriya ta fitar mai ɗauke da sa hannun mataimakin kwanturola Janar E. I. Edorhe a madadin shugaban hukumar ta Kwastam Hameed Ali, iyakokin sun haɗa da kan iyakar Idiroko a jihar Ogun, kan iyakar Jibiya a jihar Katsina, Kamba iyaka a jihar Kebbi da Ikom iyaka a jihar Ribas.

Sanarwar mai taken, ‘Sake buɗe wasu ƙarin iyakokin Nijeriya huɗu da aka gani, ta ce, “bayan umarnin shugaban ƙasa na ranar 16 ga watan Disamba, 2020, na ba da izinin sake buɗe kan iyakokin ƙasa a wurare; Iyakar Mfum, Seme, Illela da Maigatari a faɗin ƙasar nan, an umurce ni da in sanar da ku cewa an amince da wasu ƙarin kan iyakokin huɗu da aka jera a ƙasa domin sake buɗewa.

“Idiroko kan iyaka, Jihar Ogun (Yankin Kudu maso Yamma); Jibiya bakin iyaka, Jihar Katsina (Shiyyar Arewa maso Yamma); Kamba iyaka, Jihar Kebbi (Shiyyar Arewa maso Yamma); da mashigin iyakar Ikom, Jihar Kuros Riba (Yankin Kudu amso Kudu).

Shugaba Buhari a shekarar 2019 ya ba da umarnin rufe wasu iyakokin Nijeriya a wani dogon ƙoƙari na bunƙasa noman shinkafa a Nijeriya.

A wancan lokacin, babban kwanturolan hukumar kwastam ta Nijeriya Hameed Ali, ya sanar da cewa, “babu lokacin da za a sake buɗe iyakokin, wanda zai cigaba da kasancewa a rufe har sai mun sami cikakken iko kan abin da ke shigowa”.