Masu tallata kaya na Afirka za su gabatar da kayayyaki masu kyau a yanar gizo

Daga CRI HAUSA

Za a shirya “Bikin sayar da kaya masu alamomi da inganci ta yanar gizo karo na huɗu, kuma bikin sayar da kaya masu kyau na Afirka” a tsakanin ranakun 28 ga watan Aflilu zuwa ranar 12 ga watan Mayu. Bisa ƙididdigar da aka yi, shagunan sayar da kayayyaki ta Intanet fiye da 300 za su halarci bikin, kuma za a samu halartar samfurori sama da 100,000, da ‘yan kasuwa fiye da miliyan ɗaya. Ana sa ran masu sayayya za su ɗanɗana kofi na Habasha, da miyar yaji ta Ruwanda, da ganyen shayin Kenya, da dai sauransu ta hanyar watsa shirye-shirye kai tsaye da jakadan su ke yi ta yanar gizo.

A cikin ‘yan shekarun nan, sabon tsarin kasuwanci kamar sayayya ta yanar gizo yana haɓaka a Afirka, kamfanoni da ɗaiɗaikun jama’a na Afirka suna fatan koyon fasahohin da ƙasar Sin ta samu a fannin bunƙasuwar fasahar zamani, da ƙarfafa haƙiƙanin hadin gwiwarsu da ƙasar. Zhou Ping, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, ya ba da wasu alkaluma. Ya ce, a shekarar 2021, yawan kuɗin da aka samu na cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ya ƙaru duk da yanayin da ake ciki na tinkarar annobar COVID-19, inda ya karu da kashi 35.3%, wanda ya kai matsayin da ba a taɓa samu ba a tarihi. Daga cikinsu, shigo da kayayyaki daga Afirka ya karu da kashi 43.7%.

Zhou ya ƙara bayyana cewa, “Ƙasar Sin ba ta taba neman rarar ciniki a yayin cinikayyarta da Afirka ba. Bisa aiwatar da matakai kamar su samar da sauki wajen shigo da kayayyakin amfanin gona na Afirka, da faɗaɗa fanonnin da ba za a biya harajin kwastan ba, da bukukuwan sayayya ta yanar gizo da dai sauransu, za a sa kaimi da faɗaɗa shigo da kayayyakin Afirka a ƙasar ta Sin, da ciyar da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka gaba cikin daidaito kuma mai inganci. A sa’i ɗaya kuma, kayayyaki masu inganci na Afirka su ma za su bayar da zaɓi iri daban-daban ga masu sayayya na ƙasar Sin. Na yi imanin cewa, ko shakka babu, bikin sayar da kayayyaki masu kyau na Afirka ta Intanet na bana zai kasance mai ban mamaki, wanda zai ba da muhimmiyar gudummawa wajen inganta haɗin gwiwar Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi.”

Mai fassara: Bilkisu Xin