An yi garkuwa da hadima Ramatu Abarshi a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Masu garkuwa sun yi garkuwa da fitacciyar hadimar nan mai taimakon al’umma, Ramatu Sangei wacce aka fi sani da Ramatu Abarshi a Kaduna bayan da ta kammala shirin taimaka wa wasu marayu.

Ramatu tsohuwar matar Marigayi Air Commodore A. Abarshi ce kuma shugabar ƙungiyar nan mai zaman kanta ta Barkindo Rahama Initiative (BRAIN), ƙungiyar da ta shahara wajen taimaka wa mata da matasa da marasa galihu.

Ramatu a bakin aiki

Al’amarin ya faru ne a ranar Juma’a inda aka sace Ramatu tare da ‘yarta Amira Aliyu Abarshi da sakatarenta Injiniya Ibrahim Suleiman.

Majiya ta kusa da ‘yan’uwan waɗanda lamarin ya shafa ta ce, lamarin ya faru ne kusa da Kasuwan Magani da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna bayan da ta kammala rabon tallafi ga marayu da wasu marasa galihu a yankin Tilde Kargiji cikin Ƙaramar Hukumar Lere a jihar.

“Suna kan hanyarsu ta komawa Kaduna ne hakan ta faru. Muna fata ku saka su cikin addu’o’inku a wannan wata mai alfarma don samun ‘yancinsu,” in ji majiyar.

Jaridar Neptune Prime ta ce masu garkuwar sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako su.

Ya zuwa haɗa wannan labari wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna amma hakan ya ci tura.