Japan, ki yi hattara!

Daga CRI HAUSA

Yau da shekara guda da ta gabata, gwamnatin ƙasar Japan ta sanar da ƙudurinta na zubar da dagwalon ruwan tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku. A kwanan nan kuma, kamfanin samar da wutar lantaki ta Tokyo, wato Tokyo Electric Power, ya kare aniyarta na fara gina mafitar dagwalon ruwa a ƙarƙashin teku, ba tare da yin la’akari da nuna adawa ko kuma rashin amincewar da gamayyar ƙasa da ƙasa, da ma al’ummar ƙasar suka nuna ba. An ce, za a fara zubar da ruwan a farkon shekarar 2023.

Sakamakon igiyar ruwa mafi ƙarfi da ake samu a mashigar tekun Fukushima, an ce da zaran an zubar da ruwan, zai iya yaɗuwa zuwa sama da rabin tekun Pasifik cikin kwanaki 57, da ma tekunan duniya baki ɗaya cikin shekaru 10. Ba za a iya kawar da kai daga mummunan tasirin da zai iya haifarwa ga yanayin teku da ma tsaron abinci da kuma lafiyar bil Adama ba. Zubar da dagwalon ruwa ba batu ne da ya shafi ƙasar Japan ita kadai ba, sai dai batu ne da ya shafi duniya baki ɗaya. Japan, ki guji ɗaukar mataki na son kai!

Mai Zane: Mustapha Bulama