2023: Malam Ibrahim Khalil bai faɗi zaɓe ba!

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Sau da yawan lokaci ana kallon wanda ya lashe zaɓe a matsayin wanda ya yi nasara, sannan sau da yawan lokacin ana kallon wanda ya faɗi zaɓe a matsayin wanda ya yi rashin nasara.

Ni kuwa sam ba haka na ke kallon lamarin ba, ina duba na tsanaki in kalli lamura da dama, cikin wannan lamari kuwa ina kallon Malam Ibrahim Khalil a matsayin wani gwarzo wanda ya fi kowa cin nasara a zaɓen Gwamnan Kano na 2023.

A wani salo da ba a saba da shi ba, tun daga 1999 zuwa 2023, shi ne a ga Malami na musulunci katafare mai ba da karatu da wa’azi bisa munbari ya tsunduma harkar siyasa, har ya tsaya takarar Gwamna, ba wai ya tsaya ya yi ta bambaɗanci ga ‘yan siyasa idan an kafa gwamnati a ba shi kujerar je ka na yi ka ba, wato “appointment”

Shi ya yarda ya fito ƙarara ya yi siyasarsa ya yaɗa manufarsa a zahiri, ba wai kawai yai ta halartar tarukan shan shayin da ƙungiyoyi ke ta shiryawa ai ta dogon turancin yadda lamura suka lalace a al’umma ba, ba tare da komai ya canza ba shekara da shekaru.

Malam ya fuskanci cewa dole mutanen kirki su shiga siyasa da niyyar kawo canji, don tabbas a yanzu dai ta hanyar siyasa ce muke fatan kawo canji da ake fata, Malam ko bai ja da baya ba, ya fuskanci gwagwarmaya ba a iya mumbarin karatu da tarurruka a rufaffen waje ta tsaya ba, hasali ma, za mu ce iya cewa a yanzu gwagwarmayar gaskiyar canza lamura tana farawa ne daga lokacin da mutanen kirki suka fito filin dagar siyasa don siyi mubazara da baragurbin azzalamun mutanen da suka daɗe suna zaluntar al’umma.

Duk da raunin ƙarfin jam’iya, da rashin kuɗi, da rashin goyon bayan da yawan wanda ake ganin ya kamata su dafa wa tafiyar Malam, hakan bai sa ya gaza ba, haka tafiyar da aka kafata a kan manufa take, ba a ja da baya.

Cikin wani salo mai burgewa, Malam ya gabatar da salon kamfen ɗinsa ba ‘yan jagaliya, ba harmagaza ba watsi da kuɗi da tashanci, ba cin mutunci da aka saba gani a siyasa.

Haƙiƙa Malam Ibrahim Khalil ya nuna wa mutanen kirki cewa su ma za su iya shiga siyasa a dama da su. Yanzu ko ba komai an daina cewa mutane kirki sun ƙi shiga siyasa, sai dai a ce mutanen kirki sun fifita jam’iyarsu fiye da mutanen kirkin da suka shiga siyasa.

Malam Ibrahim Khalil ya cika tauraron da ya yi dai-dai da sunan littafin tarihin rayuwarsa da aka rubuta mai suna “The Practice of Knowledge” ƙwarai! Ilimi yana da muhimmaci, amma amfani da shi a lokacin da ake buƙatar hakan ne mafi muhimmanci!

A fahimtata Malam Ibrahim Khalil bai faɗi wannan zaɓen ba, kawai dai bai samu mafi rinjayen ƙuri’u ba, wannan ko ba laifinsa ba ne. Sai da ya kafa wani lamari da zai ƙarfafi mutanen kirki nan da shekaru masu zuwa.

Ƙila da za a tambayeni, a zaɓen 2023 me na yi nadamar ƙin yi, ba tare da dogon tunani ba zan ba da amsa kamar haka: “Rashin shiga tafiyar Malam Ibrahim Khalil”

Mukhtar Mudi Sipikin, madubuci kuma ɗan siyasa nai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga Kano.