Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Falsafa ta a siyasa ita ce: “Kar ka taɓa son wani ɗan siyasa, sai aikin alherinsa; haka kuma, kar ka tava ƙin ɗan siyasa, sai aikin sharrinsa”. Wannan dalilin ya sa a 2019, sakamakon badaƙalar Ganduje muka yi caa! da Jan hankalin Kanawa cewa ba mu cancanci shugaba haka ba.
Amma sai aka wayi gari “Mai gaskiya” a sama, ya ɗaure gindin rashin gaskiya a ƙasa. Duk da kamfen ɗinmu ya karɓu a wajen al’umma an fito an ka da gwamnati, sai Inconclusive ya ƙwace nasarar ƙiri-da-muzu.
Kwankwaso ya yi rawar gani wajen ƙin tunzura magoya baya kuma aka karɓi ƙaddara. Ina kyautata zato Allah ya dubi wancan dattako da ya nuna, da haƙurin Kanawa wajen haɗiye baƙin ciki, domin akwai banbancin a zafin an kayar da kai zaɓe, da kuma banbancin ka ci zaɓen a qwace maka, aka jira shekaru huɗu.
Allah Gwani ne na hisabi, domin da ya tashi yin sakayya, a duk cikar APC sai aka rasa waɗanda za a bai wa takara face waɗanda suka yi ta’addancin da ya kawo tsaiko a zaɓen Gama (Gawuna da Garo) abinda ya haifar da INCONCLUSIVE kuma suka karɓe zaɓe. Amma sai Allah ya zaɓo su a APC domin cikar hisabin, yadda a rana irin ta yau sai gashi an wayi gari Abba Kabir ya kayar da su ya zama gwamnan Kano, abinda suke ta hanƙoron. Wannan babban darasi ne ga duk wani mai tsoron Allah ya gane cewa duk wata isa, ƙarfin iko ko wayo da tsageranci baya ba da mulki. Allah dai shi ne tutiyal mulk.
Ina taya Kanawa murnar wannan babbar nasara domin ba nasarar Kwankwaso ko Abba ba ce. Tarihinmu ya nuna cewa tun daga Jamhuriyya ta 2, Kanawa na canza masu mulki da ƙarfin ƙuri’a domin munga yadda Gwamna Rimi ya faɗi zaɓen 1983. Kabiru Gaya ya kayar da Magaji Abdullahi a 1992. Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003. Kwankwason ya ka da jam’iyya mai mulki a 2011.
Wannan gwaninta ta siyasarmu ta yi yunƙurin ɗorawa a 2019, amma aka daƙile ta. Amma sakamakon jajircewa irin ta kanawa sai ga shi a 2023 wannan ɗabi’a ta siyasarmu ta dawo daram. A ganina wannan ita ce babbar nasararmu, ba kawai cin Abba Gida-gida ba. Nasara ce ga ‘yanci da siyasa da al’ada, nasarar kowa ce, har Gawuna da Garo da suka faɗi a yau, domin Idan Abba ya gaza, suna iya dawowa a 2027.
Allah ya ce mana idan muka gode wa ni’imarsa sai ya ƙara mana, wanda kuma duk Allah ya ni’imta amma bai gode ba, da sannu azabar Allah za ta riske shi. Kamar yadda duk da ƙwace zaɓen 2019, maimakon APC ta kyautata wa kanawa, sai aka buɗe sabuwar sharholiya tare da ƙuntatawa al’umma da yin abubuwa, a kalmar Madugu na “Rashin daraja”.
Ba a tava qazantar mulki ba irin ta waɗannan shekaru huɗu a mulkin Kano. Malamai marasa daraja sun kasa faɗa wa masu mulki gaskiya, sun ɓige da zama kakakinsu. Duk filayen jiha an siyar da su. A baya-bayan nan daf da zaɓe mun ga yadda Allah ya taimaka aka daƙile yunkurin siyar da Filin golf na Kano Club, fili tilo da ya rage mana a matsayin lambu.
Abba Kabir, zaɓaɓɓen gwamna, ina fatan cewa shekarun 2019-2023 ba wani Bakano da ya cancanci wa’aztuwa da cewar mulki yana da iyaka, kuma aikinka shi ne hisabinka, sama da kai domin da kai Allah ya nuna mana aya. Muna kyautata maka zato, sanin cewa kai ne ginshikin ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta bijiro da su a 2011-2015.
Don haka a yanzu da kai ne wuka-da-nama, muna tsammanin ka zarta haka. A baya kun gina dubban azuzuwa amma ba kayan aiki, ba walwalar malamai. Dole a yi haka idan ana son farfaɗo da ilimi. Kun yi gadar sama, abinda ya zama wani abin kwaikwayo da ma’auni ga gwamnoni a Arewa. Yanzu ba lokacin gina gada ba ne, lokaci ne na gina masu hawa gadar.
Kwankwaso a baya ya gaza wajen kashe biliyoyi a zangonsa na biyu, ba tare da saka jari a hanyoyi da za su samarwa jiha kuɗaɗen shiga ba (musamman a harkar noma). Wajibi idan kana son nasararka da ta Kanawa ta ɗore, dole ne ka cire mu daga jerin jihohi almajirai, waɗanda kullum kokonsu a hannu sai karshen wata a garzaya Abuja a samo ‘yar tsaba.
Da zarar an biya albashi (kusan biliyan 10) sai kaga an yi wawason ragowar an zuba aljihu sannan a hari watan gaba. Wallahi Kano ta fi ƙarfin haka idan akwai shugabanci mai hangen nesa. Kano na iya samar da kuɗaɗen shiga da ba sai ta jira allocation ba. Misali, Dam-dam sama da 16 a Kano wallahi za su iya samar da biliyoyin daloli ba naira ba ga gwamnati.
A noman kifi kawai a waxannan Dam ɗin, Kano na iya karɓar cinikin Dala biliyan biyar a duk shekara na kifin da ake shigowa da shi Najeriya. Kuma harka ce da bata buƙatar wani gagarumin jari. Kuma ana iya noma tsawon shekara na tsaba (alkama, shinkafa) da musamman kayan marmari (shi ne ma logon jam’iyyarku ai). Baya ga samar da lantarki, musamman ganin yadda sabuwar dokar kasa ta sahale wa jihohi yin hakan.
Kada ka maida hankali wajen cewa sai ka taɓa komai, da zarar ka jajirce wajen samarwa Kano hanyar kuɗaɗen shiga, ka ci kashi hamsin na ƙalubalenka. Ka guji kuskuren Kwankwaso wajen yin ayyuka irin na rukunin gidajen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo. Ka ga dai idan ka ɗauke Abuja, duk Najeriya babu inda ake da rukunin gidaje irinsu.
Rashin tsari wajen ƙirƙira da aiwatar da aikin, musamman na rashin la’akari da ɗorewa, dubi irin asarar da ya jawo wa Kanawa. Wata shawarar gare ka shi ne ka lalubo makusanta waɗanda suka sanka ka sansu, waɗanda za su iya kallon ƙwayar idonka su gaya maka gaskiya ba tare da tsoro ba.
A ƙarshe Kwankwaso ya kamata ya yi la’akari da cewa duk yadda ya kai dai horar da kai, bai kai yadda ya horar da Ganduje ba amma aka wayi gari sun yi hannun riga. Ya kamata ya sakar maka mara, ya zama uba ga kowa.
Sannan kada ka manta cewa Kanawa ne ke binka bashi daga yau, domin an yi maka iya halarci, kuma ɗan halal shi ne ke rama halarci da halarci. Allah ya ba ka ikon biyan bashi kuma ya ƙare ka maimaita kura-kurai irin na Kwankwaso da Ganduje. Allah ya taya ka riƙo, mai girma zaɓaɓɓen gwamna.