Daga BASHIR ISAH
Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yarda cewa gwamnatin APC ta gaza, amma ya roƙi ‘yan Nijeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa dangane da gwamnatin ta APC.
Tinubu ya yi wannan roƙo ne yayin da yake jawabi a wajen taron jana’izar mahaifiyar Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, Grace Akeredolu, ranar Lahadi a Majami’ar Cathedral da ke Imola a yankin Owo.
Taron wanda ya samu halarcin jiga-jigan ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, gwamnoni da sauransu.
A jawabinsa, Tinubu ya gode wa Allah kasancewar ana raye tare da nusar da ‘yan ƙasa akwai yiwuwar a ga rauni da rashin iya cika burin jama’a a kan gwamnati.
“Duk da haka kada ku yanke tsammani daga gare mu, za mu yi fiye da yadda kuke zato. Za mu ƙoƙarta wajen samar da cigaban da kuke buƙata,” inji Tinubu.
Tun farko da yake nasiha a wajen taron, Rabaran Stephen Ayodeji Fagbemi ya ce, “Talakawa na ƙara talaucewa. Nijeriya buƙatar canji da zai tabbatar da kariya da tsaro a ƙauyuka.”
