Daga BASHIR ISAH
‘Yan bindiga sun nemi a biya su Naira miliyan 10 kafin su miƙa gawar Obadiah Ibrahim wanda suka yi garkuwa da shi makonnin baya a Jihar Kaduna.
A cewar majiya ta kusa da marigayin, tun farko sai da ‘yan fashin dajin suka karɓi Naira miliyan N3 daga wajen ‘yan uwa ba tare da sun sake shi ba.
Wani ɗan uwan marigayin, Kefas Obadiah, ya ce tun ranar Litinin da ta gabata Allah Ya yi wa ɗan uwan nasa cikawa amma sai a ranar Alhamis aka sanar da su.
Ya ce ɓarayin sun ƙi sakar musu gawar ɗan uwansu duk da sun karɓi fansar miliyan N3.
Ya ƙara da cewa, a farkon watan Oktoba aka yi garkuwa da ɗan uwansa a yankin Sabon Gaya a kan hanyarsa ta dawowa daga Abuja.
“Da farko sun nemi a biya fansar miliyan N200 amma daga bisani aka tsaya a miliyan N3 da ɗoriya,” in ji shi.
Kazalika, ya ce bayan haka, ‘yan bindigar sun sake karɓar miliyan N5 da babur ɗaya daga hannunsu, kuma hakan bai sa sun sako ɗan uwansu ba.
Ya ce, sai a ranar Alhamis da ta gabata suka sanar da su cewa ɗan uwansu ya mutu, kuma ba za su saki gawarsa ba sai an biya su miliyan N10, saboda wai ba za su yi musu aiki a banza ba.
‘Yan bindigar sun yi iƙirarin ‘yan sanda sun kama tare da kashe musu ‘yan uwa wannan ya sa su ma suka ɗauki fansa a kan Ibrahim.
