2024: Nasarawa, Bayelsa da Oyo su zama koma-baya wajen aiwatar da kasafin kuɗi – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani rahoto da wata ƙungiya mai sa ido kan kasafin kuɗi ta BudgIT ta buga, ta sanya Oyo, Bayelsa da Nasarawa a matsayin jihohin da suka gaza wajen fi aiwatar da kasafin kuɗi a ƙarshen shekarar 2024.

Jihohin uku sun samu maki 69, 73 da 75.

Ekiti, Kaduna, Adamawa, Benuwai, Ebonyi, da Edo an saka su a matsayin kan gaba da maki 100, 100, 98, 97, 97, 97.

Babu jihar da ta samu ƙasa da kashi 40 cikin 100. BudgIT ta bayyana cewa hakan na kawo ci gaba ga fayyace gaskiya a kasafin kuɗi a tsakanin jihohin Nijeriya.

Don cimma wannan matsaya, BudgIt ta binciki kasafin kuɗin da aka amince da su.

Fahimtar inda kuɗaɗen ke tafiya zai tabbatar da ayyukan gwamnati ga jama’a.

Ya ƙunshi yadda gwamnatoci ke tarawa, kashewa, da sarrafa dukiyoyin jama’a, tare da cikakken bayani a kan duk kadarorin jama’a.

By ukarofi