Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alamu sun nuna cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu na shirin saka ƙafar kwando ɗaya da wasu ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya kan gazawa wajen bin ƙa’idojin kwangila.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ministocin suka buƙaci a ƙara musu kuɗi, gabanin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda shi ma shugaban ƙasar ya dage.
Idan za a iya tunawa, a farkon shekarar nan ne Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗi na kusan Naira Tiriliyan 55, wanda shi ne mafi girma da kowane Shugaban Nijeriya ya aiwatar.
A wani yunƙuri na wajen aiwatar da kasafin kuɗin, majalisar zartarwa ta tarayya FEC, ta amince da kasafin a taronta na ƙarshe.
Sai dai gwamnatin ta bayar da umarnin a ci gaba da kasafin kuɗin shekarar 2024 har zuwa watan Yuni na wannan shekara, lokacin da kasafin 2025 zai fara aiki gadan-gadan.
An tattaro cewa, a cikin wani sabon yunƙuri na tabbatar da aiwatar da kasafin kuɗi a kan kari, Debo Adebowale Adedokun, Darakta Janar na BPP, ya dage cewa dole ne a kammala dukkan hanyoyin sayen kayayyaki a ƙarshen shekara.
Biyo bayan gazawar shugabannin ma’aikatu na bin ƙa’idojin da aka ƙayyade a ƙarshen watan Maris, George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya SGF, ya fitar da wata sanarwa, inda ta canja lokacin.
Ya ƙara wa’adin kammala dukkan tsare-tsaren saye da sayarwa zuwa ranar 30 ga Afrilu, 2025.
Ministocin a wani taron majalisar zartarwa ta tarayya FEC na baya-bayan nan, sun buƙaci a ƙara yawan ma’auni kuma an kafa kwamitin da zai duba matakin da aka amince da shi a shekarar 2023.
