Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kwamitin Kula da Asusun Al’umma na Majalisar Wakilai ya umarci Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da ta dawo da kuɗaɗen da suka kai Naira biliyan 33,563,469.10 zuwa asusun Gwamnatin Tarayya, bayan ta gano cewa an kashe kuɗaɗen ne wajen tafiye-tafiyen ƙasashen waje ba tare da izini ba.
An bayar da umarnin ne a ranar Litinin yayin zaman kwamitin da Bamidele Salam ya jagoranta kan rahoton babban mai binciken kuɗi na 2021.
Binciken ya nuna cewa an biya wasu jami’an ma’aikatar guda uku dala 3,000 kuɗaɗen alawus-alawus na tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Kenya, Afirka ta Kudu, Maroko, Girka da Faransa ba tare da wani izini ko takardun da suka nuna yadda aka yi amfani da kuɗaɗen ba.
Wannan matakin ya kasance wani ɓangare ne na badaƙalar kuɗaɗen da aka bankaɗo a asusun ma’aikatar, yayin da rahoton binciken ya taso da manyan tambayoyi biyar a kan ma’aikatar sufuri.
Waɗannan sun haɗa da rashin samar da bayanan kashe kuɗaɗen ma’aikata da ya kai N1,089,848,974.00; ba bisa ƙa’ida ba na N400,177,312.00 zuwa bankin shigo da kaya na Nijeriya (NEɗIM); kuɗaɗen da ba a tabbatar da su ba na shirye-shiryen horarwa da suka kai N93,539,100.00; kuɗaɗen balaguron ƙasa da ƙasa ba tare da izini ba na N68,591,119.00; da bayar da kwangilolin da suka kai N11,120,000.00 ba tare da bin ƙa’idojin da suka dace ba.
An gabatar da ƙudirin kƙwato kuɗaɗen nan take inda Hon. Olusola Fatoba da Hon. Amobi Godwin tare da kwamitin suka buƙaci a mayar da kuɗin da suka kai N33,563,469.10 da aka biya, da sarrafa biza, kuɗin jirgi ba tare da amincewar da ya dace ba da kuma shaidar yadda aka yi amfani da alawus ɗin na dala 3,000.
Kwamitin ya kuma buƙaci a biya N11,120,000.00 da aka bai wa Cibiyar Fasahar Sufuri ta Nijeriya, NITT, domin horar da ma’aikata 78.
