2027: Abin da ya sa zan dawo da tallafin fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba, inda ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur a farko ba, amma matsalar ita ce yadda gwamnati ta yi amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin. Ya ce ya kamata kuɗin da aka samu daga cire tallafin su taimaka wajen rage talauci, ingantailimi, magance matsalar tsaro da kuma samar da damammaki ga matasa.

Atiku ya ce, “Ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma ina kuɗin? Ina kuɗin da aka samu? An yi niyyar amfani da su wajen rage talauci da taimaka wa yara su samu ilimi. Ina

kuɗin yanzu? Kamar ana satar su ne.” Ya ƙara da cewa idan aka zaɓe shi a 2027, zai dawo da tallafin man fetur, tare da ɗaukar matakan tabbatar da cewa duk wanda ya saci kuɗin gwamnati ya mayar da su.“Idan aka zaɓe ni, zan dawo da tallafin man fetur, kuma duk wanda ya saci kuɗin dole yamayar da su,” inji Atiku.

Sai dai wannan matsaya ta Atiku ta bambanta da matsayinsa a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, lokacin da ya goyi bayan cire tallafin man fetur. A wancan lokacin, Atiku ya yi alƙawarin cewa zai cire tallafin cikin kwanaki 100 na farko idan aka zaɓe shi, yana mai cewa tsarin tallafin ba zai ɗore ba kuma ya kamata a yi amfani da kuɗin da aka samu wajen inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023, jim kaɗan bayan rantsar da shi. Cire tallafin ya haifar da tashin farashin man fetur, tare da ƙarin tsadar sufuri da kayayyaki, lamarin da ya ƙara tsananta matsin tattalin arziki da ’yan Nijeriya ke fuskanta. Atiku ya ce bai sauya ra’ayinsa gaba ɗaya kan cire tallafin ba, sai dai yana ganin matsalar ita ce rashin ganin amfanin kuɗin da aka samu bayan cire shi.

Ya ce da an yi amfani da kuɗin yadda ya kamata wajen bunƙasa tsaro, ilimi da samar da ayyukan yi da damammaki ga matasa, da ba a samu irin wannan matsalar ba. A cewar Atiku, gwamnatin da zai jagoranta za ta tabbatar da cewa duk wani kuɗin da aka samu daga irin wannan sauyi an mayar da shi ga abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

A nasa ɓangaren, Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke kula da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu ƙarin albarkatun kuɗi na Naira tiriliyan 15.8 tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025 sakamakon cire tallafin man fetur. Sai dai har yanzu ana ci gaba da muhawara kan ko ƙarin kuɗin da gwamnati ta samu ya haifar da ingantaccen sauyi a rayuwar ’yan Nijeriya, musamman wajen rage tsadar rayuwa da talauci.

By ukarofi

Leave a Reply