2027: Ba sai ka zo kamfen ba, ba abokin hamayya a Kogi – Yahaya Bello ga Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai buƙaci yin kamfen don zaɓen 2027 a jihar Kogi ba.

Da yake magana a ranar Asabar yayin taron jam’iyyar APC a Kogi, Bello ya ce jam’iyyar ba ta da kowace irin hamayya a jihar, wadda ke Arewa ta Tsakiya.

Tsohon gwamnan ya bayyana jihar Kogi a matsayin garkuwa ga jam’iyyar mai mulki, yana mai cewa Shugaba Tinubu yana da gagarumin goyon baya daga jama’a a dukkanin sassan jihar.

“Mai girma Shugaban ƙasa, ba ma sai ka zo jihar Kogi don yin kamfen a 2027 ba. Kada ka wahalar da kanka da cewa kana son zuwa Kogi don neman wa’adi na biyu. Babu wata jam’iyyar hamayya a jihar Kogi”, inji Bello.

Ya ƙara da cewa “Waɗanda suke ta hayaniya a wani wuri ba su taɓa ganin zakin ba. Murna gare ka Shugaban ƙasa. Kowace ƙasa mai girma tana da shugaba wanda kowa yake karkata zuwa gare shi.”

Ya cigaba da cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kai ne wannan shugaba da za mu ci gaba da karkata zuwa gare ka har bayan wa’adinka na biyu.”

Kazalika, Bellon ya kuma yaba wa jagorancin Tinubu da ƙoƙarinra wajen inganta harkar tsaro, faɗaɗa ababen more rayuwa da tabbatar da ƙarin kuɗaɗen kasafi ga jihohi.

By Babaji