Sanata Wamakko ya ba NABTEB kyautar babban ofishi a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bada kyautar ginin ofis ga Hukumar shirya jarabawar NABTEB, domin ƙarfafa ci-gaban ilimi da bunƙasa matasa a jihar.

Sanata Wamakko, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙetare, ya miƙa ginin na bene ga Sakataren NABTEB, Dakta Aminu Muhammad, a yayin bikin ƙaddamarwa da aka gudanar a Birnin Sakkwato a jihar.

Ƙaramin Ministan Ayyuka, Alhaji Bello Muhammad Goronyo ne ya wakilci Sanatan a wajen bikin, inda ya bayyana cewa gudunmawar na daga cikin irin goyon bayan da Wamakko ke bayarwa ga ci-gaban harkar ilimi, matasa da tattalin arziƙin al’umma.

Ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da manufar ‘Renewed Hope Agenda’ ta Shugaba Bola Ahmad Tinubu da kuma ‘Smart Agenda’ ta Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, waɗanda ke mayar da hankali kan haɓaka ilimi, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

Kazalika, ya ce makomar Nijeriya tana cikin ilimin fasaha da sana’o’i, domin duniyar yau na buƙatar ƙwarewa ta zahiri fiye da takardun karatu.

Da yake jawabi, Sakataren NABTEB, Dakta Aminu Muhammad, ya bayyana cewa wannan gudunmawa ita ce irinta ta farko da wani mutum ya taba yi wa hukumar tun farkon samar mata da ofishi a jihar.

Ya kuma yaba wa Sanatan bisa kishin ƙasa da jajircewarsa wajen tallafa wa ci-gaban ilimi da matasa.

Har’ilayau, ya ce sabon ginin zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar da samar da ingantacciyar hidima ga ɗalibai da ke rubuta jarrabawar NABTEB.

By Babaji