Kotu ta haramta gangamin sako Nnamdi Kanu da Sowore ya shirya a wasu yankunan Abuja

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta bada umarnin hana Omoyele Sowore, mai gidan jaridar Sahara Reporters, da wasu masu fafutuka yin zanga-zanga a wasu wurare a Abuja, ciki har da Fadar Aso Rock, domin neman a sako Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB da aka haramta.

Mai shari’a Mohammed Umar ne ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a bayan lauyan ‘yan sanda, Wisdom Madaki, ya gabatar da ƙarar gaggawa a madadin Gwamnatin Tarayya (FRN).

A cewar kotun, an haramta yin zanga-zanga a wurare kamar Aso Rock Villa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Hedikwatar ‘Yan Sanda, Kotun Daukaka Kara, Eagle Square, da kuma Shehu Shagari Way, har sai an saurari ƙarar da aka shigar gaba ɗaya a ranar Litinin, 20 ga Oktoba, 2025.

Kotun ta kuma umarci cewa a sanar da Sowore da sauran wadanda ake ƙara da takardun umarnin kotu kafin ranar da aka ƙayyade domin sauraron ƙarar.

An bayyana cewa Sowore, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar African Action Congress (AAC) a shekarun 2019 da 2023, yana shirin shirya zanga-zangar lumana don neman a saki Nnamdi Kanu, wanda ake tuhuma da laifin ta’addanci a gaban kotu.

Saidai wannan umarni ya zo ne bayan jami’an tsaro sun nuna damuwa da yiwuwar tashin hankali a wuraren da aka tsara gudanar da zanga-zangar.

A ranar Litinin za a cigaba da sauraron shari’ar.

By Babaji