Daga MUKHTAR YAKUBU
A yanzu dai za a iya cewa masana’antar fina-finai ta Kannywood ta na ƙara ci gaba kusan kowanne lokaci saboda yadda harkokin kasuwancin fina-finan suke bunƙasa a duniya tun daga lokacin da harkar ta koma onlayin.
An samu damar buɗe tashoshi da dama da aka rinƙa saka fina-finan domin kallon su a duniya, wanda hakan ya bayar da damar duk inda mutum yake a duniya kallon finafinan ba zai yi masa wahala ba, don haka ne ake samun masu bibiyar fina-finan kullum suke ƙaruwa.
Baya ga haka su kansu masu gudanar da harkar sun yarda inganta sana’ar su tana da muhimmanci, don haka ne a yanzu duk wanda zai yi harkar to ya kan yi ƙoƙari ya samar da kayan aikin da zai inganta fim ɗin don ya zama ya samu karɓuwa a wajen masu kallo.
‘Ƙudiri’ sabon shirin fim ne mai nisan zango wanda ya sha bamban da waɗanda ake kallo. Shiri ne da aka zuba basira da lissafi wanda yake ƙunshe da zunzurutun fikira kamar irin fina-finan da suka yi suna a duniya na ƙasashen ƙetare.
Ƙwaƙwalwa ta taka muhimmiyar rawa a shirin, yayin da masu laifi suka aikata kisan kai suka toshe duk wata hujja da za a gano su, a lokacin su kuma ƙwararrun jami’an tsaro suka zurfafa bincike cikin ƙwarewa.
Ganin yadda aka zuba basira da kwarewa a aikin musamman ma dai shi furodusan Isah Bawa Doro da ya kasance mai himma da ƙwazo ya sa fim ɗin ya zo da wani sabon salon da ya tafi da tunanin masu kallo.
Fim ɗin ‘Ƙudiri’, yana tafiya ne cikin sarƙaƙƙen labarin da idan ka fara kallon sa ba za ka daina ba, don haka idan ka kammala kallon na wannan makon za ka shafe mako guda cike da zumuɗi da ɗokin Alhamis ta zagayo domin ci gaba da kallon inda aka tsaya.
Sababbin fuskoki ne a cikin shirin amma saboda ƙayatuwarsa ya kafa tarihin da babu sabon shirin da ya taɓa kafawa. Inda ya sami mabiya sama da miliyan ɗaya cikin kwana huɗu kacal. Tabbas ‘Ƙudiri’ ya kama hanyar da zai danne duk wani shiri mai dogon zango da yake tashe a duniyar finafinan Hausa. Domin shiri ne da ya zo da sabon salon da ba a taɓa ganin irin sa ba,. Ya zo da darusan rayuwa mabambanta. Shiri ne da hatta jami’an tsaro sai sun ƙaru da ilmin cikinsa na bincike, basira, fikira da lissafi balle kuma sauran jama’ar gari.
Da a ce ana shiri irin na ‘ƙudiri’ da Kannywood ta yi zarra a duniyar fina-finai ta duniya, domin mafi yawancin shirye-shiryen Kannywood ana yinsu ne kan soyayya, shaye-shaye ko daba. Amma shi ‘Ƙudiri’ na daban ne ya zo da wani salo da yake wahalar bayyanawa a baki dole sai mutum ya gani da kansa zai fahimta.
