Hrithik da wasu manyan jaruman Bollywood sun maka fasahar AI kotu

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Rahotanni daga Times of India sun ruwaito cewa, wasu shahararrun taurarin Bollywood, ciki har da Hrithik Roshan, sun je Kotun Babbar Delhi domin neman kariya daga amfani da fasahar artificial intelligence (AI) wajen ƙirƙirar abubuwa kamar hotuna, bidiyo ko sauti da ke amfani da sunayensu, muryoyinsu ko siffofinsu ba tare da izini ba. 

Kotun ta bayar da umarni cewa, a cire wasu shafukan yanar gizo da ke amfani da hotuna, bidiyo ko links da aka yi zargin suna amfani da Hrithik Roshan ba da izini ba. 

An nuna cewa wannan roƙo ya biyo bayan ƙaruwa wajen amfani da fasahar “deepfake” da AI wajen ƙirƙirar abubuwan da ke kama da mutum wajen tallafi, kasuwanci ko yaɗa labarai marasa gaskiya. 

Kotu ta kuma bayyana cewa, ba za ta bayar da umarni na gaggawa (eɗ-parte) don cire fan pages ba a wannan mataki, sai bayan sun saurari ɓangarorin da abin ya shafa. 

Masanin doka kan haƙƙin mutum da fasaha, Dr. Layla Mansoor, ta ce: “A zamanin fasaha kamar yanzu, mutane suna buƙatar kariya daga amfani da hotonsu da muryoyinsu ba tare da izini ba. Wannan mataki na kotu na iya zama tushe don dokoki masu ƙarfi a nan gaba.”

Wannan nasara ta farko ga Hrithik Roshan a kotu tana nuna cewa, Bollywood da masana’antar nishaɗi sun fara ɗaukar mataki mai ƙarfi wajen kare haƙƙinsu a zamani na AI. Idan aka ci gaba da irin wannan biyayya ga dokoki, zai taimaka wajen hana matsalolin yaɗa ƙarya da ɓata suna ga taurari.

By ukarofi