Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Nijeriya, ACF ta yi watsi da kalaman da ke cewa babu wanda zai fito ya yi takara da Shugaba Tinubu a jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
ƙungiyar ta ce ‘yan arewacin ƙasar na da damar fitowa takara duk da cewa wasu shugabannin APC a yankin sun goyi bayan takarar shugaban ƙasar.
ACF, ta ce waɗannan kalamai sun saɓawa kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma irin waɗannan kalamai bai kamata su riƙa fitowa daga bakin waɗanda ake yi wa kallon yi wa shugabanni ba.
Farfesa Tukur Muhammad Baba, shi ne mai magana da yawun ƙungiyar tuntuɓar ta ACF, ya shaida wa BBC cewa, idan dai har ana dimokraɗiyya sannan ana yinta bisa yadda tsarin mulki ya tanadar a yanzu, to kundin tsarin mulkin ta gindaya wasu ƙa’idoji da ɗan ƙasa zai cika kafin ya tsaya takara.
Ya ce,”A bisa tsarin doka duk mutum in dai ɗan Nijeriya ne ba wai sai ɗan wata shiyya ko yankin ba kuma ya cika ƙa’idojin hukumar zaɓe na tsayawa takara, to zai iya tsayawa takara a duk muƙamin da yake so.”
Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce “Mu ƙungiyarmu ba wai jam’iyyar siyasa ce ba, amma muna da sha’awa akan abin da yake na mulki da kuma siyasa, mu faɗakarwace ta mu.”
Mai magana da yawun ACF, ɗin ya ce ya kamata jam’iyyar APC ta sake nazari akan wannan kalamai na ta a bawa kowa dama idan har yana son ya fito takarar shugaban ƙasa.
To sai dai kuma Malam Bala Ibrahim, daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC a Nijeriya, ya shaida wa BBC cewa, ko shakka babu kundin tsarin mulkin ƙasa ya bai wa kowanne ɗan ƙasa damar tsayawa takara muddin ya cika ƙa’idojin da suka kamata, to amma duk da haka akwai soyayya ta jam’iyya.
Ya ce,”Jam’iyya na kasancewa tana da wanda ta ke so ta tsayar ya yi mata takara wanda kuma ya cika sharudan da jam’iyyar ke so don haka sai ta basu takara.”
Malam Bala Ibrahim, ya ce “Ba wai dole jam’iyya zata hana mutane takara ba ne idan aka samu wadanda ke son takarar kuma sun cika sharudan da ake so to jam’iyya bawa kowa dama ya tallata hajarsa daga nan kuma sai tantance a zabi wanda ake gani ya fi cancanta.”
A watan Mayu ne shugabannin APC a shiyar arewa maso yammaci da suka ƙunshi gwamnoni da shugabannin jam’iyyar na kasa da jihohi da ‘yan majalisar tarayya da kuma ministoci da jiga-jigan jam’iyyarsu ma suka jaddada goyon bayansu ga Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Duk da cewa kawo yanzu shugaba Tinubu bai fito ya ce zai nemi wa’adi na biyu ba amma masana na ganin yadda ‘yan siyasa suka bige da batun zaɓe tun a yanzu, babban ƙalubale ne ga dimokuraɗiyya da kuma ci gaban Nijeriya.
