
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga editocin Nijeriya da su mayar da aikin tantancewa a matsayin jigo kuma al’ada a ɗakin yaɗa labarai, yayin da ƙasar ke fuskantar zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa fasahar AI ta zama hanyar mayar da ƙarya ta zama gaskiya acikin al’umma.
Mohammed Idris ya bayyana haka ne yayin jawabi a babban taron editoci na All Editors Conference (ANEC 2026) da aka gudanar a Enugu mai taken “The Ballot, the Media and Task of Keeping Democracy Alive” da kuma ƙaramin take “When Lies Look Real: Detecting and Debunking AI Disinformation Before, During and After Election.”
Ya ce, ingancin labarai ga ‘yan ƙasa zai yi matuƙar tasiri yayin da INEC ta shirya zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokokin Ƙasa a ranar 16 ga Junairu, 2027 da na gwamnoni da majalisun dokokin jihohi a 6 ga Fabrairu, 2027. Ministan ya bayyana cewa, ƙuri’a tana da amfani a yayin da dimukraɗiyya ta dogara da ‘yan ƙasa wajen samun sahihan labarai waɗanda da su suke iya ‘yanke hukunci kan matakan da suke ɗauka.
A cewarsa, editoci na da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen mene ne ya dace al’umma su riƙa tattaunawa akansu, yadda ake tsara al’amura da abin da ‘yan ƙasa suke gani a wayoyin hannu da kafafen sada zumunta, al’amarin ya ke fuskantar ƙalubale a yanzu sakamakon bayyanar fasahar AI. “Fasahar AI ta samar da hanyoyin haɗa hotuna, bidiyoyi, ɗaukar murya da takardun bayanai da ka iya mayar da su kamar na gaske alhalin ba haka ba ne. Za a iya samar da jawabin ƙarya ta sunan muryar wani jami’in gwamnati ce. Bidiyon da aka ƙirƙira zai iya karaɗewa cikin ‘yan mintina,” inji shi.
Idris ya ce, babban haɗarin da wannan zai haifar shi ne mutane za su koma daina yardar da dukkan abin da aka yaɗa sakamakon yaɗa labaran bogi daga fasahar da wasu ke yi, ta yadda hatta binciken ƙwaf ma sai ya riƙa fuskantar ƙalubale.
Haka kuma, ministan ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su yi amfani da irin salon horon tantance bayanai wajen ruwaito ayyukan gwamnati musamman kan muhimman ci-gaban da aka samu ta gyare-gyaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fannin tattali.
