2027: Kalubalen da tsofaffin ministocin Tinubu ke fuskantar bayan saukarsu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, wasu tsofaffin ministocin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka yi murabus daga Majalisar Zartarwa ta Tarayya domin neman muƙaman siyasa sun fara fuskantar wata sabuwar ƙalubale ta siyasa.

Abin da tun farko aka ɗauka a matsayin wata dabara ta siyasa daga manyan jami’an gwamnatin domin ƙarfafa burinsu na zaɓe, yanzu ya fara bayyana irin tsananin rikicin cikin gida, ƙarfin tsarin jam’iyya da kuma fafatawar maye gurbi a jam’iyyar APC.

Ya zuwa yanzu, mutum biyu kacal daga cikin ministoci biyar da suka ajiye muƙamansu bayan umarnin fadar shugaban ƙasa ga masu riƙe da muƙaman siyasa masu neman tsayawa takara ne suka samu tikitin jam’iyya.

Murabus ɗin nasu ya biyo bayan tanadin Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta wajabta wa masu riƙe da muƙaman gwamnati da ke son shiga zaɓen fidda gwani su sauka daga mukamansu kafin fafatawa.

Daga cikin waɗanda suka bar majalisar ministoci akwai tsohon Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, wanda ya yi murabus domin neman tikitin gwamnan jihar Bauchi; tsohon ƙaramin Ministan Harkokin Jinƙai Yusuf Sununu, wanda ya nemi tikitin sanata a Kebbi; tsohon Ministan Sufuri Sa’idu Alkali, wanda ya nemi tikitin gwamnan jihar Gombe; tsohuwar ƙaramin Ministar ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi Nkeiruka Onyejeocha, wadda ta nemi kujerar Majalisar Wakilai a jihar Abia; da kuma tsohon Ministan Wutar Lantarki Adebayo Adelabu, wanda ya shiga takarar gwamnan jihar Oyo. Sai dai duk da shahararsu da kasancewarsu tsofaffin ministoci, sakamakon siyasar nasu ya bambanta ƙwarai.

Ga Onyejeocha da Sununu, komawa siyasa bayan barin muƙamin minista ya kawo musu nasara a matakin farko. Onyejeocha ta zama ’yar takarar APC ba tare da hamayya ba a mazaɓar Isuikwuato/Umunneochi ta Majalisar Wakilai a jihar Abia.

Haka kuma Sununu ya samu tikitin jam’iyya bayan ya janye daga neman kujerar Sanatan Kebbi ta Kudu, inda daga bisani ya samu tikitin mazaɓar Yauri/Shanga/Ngaski ta Majalisar Wakilai a jihar Kebbi. Sai dai nasarorin nasu sun sha bamban da matsalolin siyasar da wasu tsofaffin takwarorinsu ke fuskanta.

A jihar Oyo, burin Adelabu na zama gwamna ya samu babban tangarɗa bayan da ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na APC a hannun Sanata Sarafadeen Alli. Tsohon ministan, wanda ya yi murabus bayan wa’adin da shugaban ƙasa ya gindaya, ya shiga takarar da fatan amfani da tsohuwar cibiyar siyasarsa domin sake neman kujerar gwamna. Sai dai sakamakon zaɓen ya bayyana irin ƙarfin rikicin cikin gida da kuma yadda yake da wahala a shawo kan manyan tsare-tsaren siyasa a cikin APC.

Bayan zaɓen, Adelabu ya yi watsi da sakamakon, yana zargin cewa an tafka kura-kurai da dama kuma sakamakon bai nuna ainihin ra’ayin ’yan jam’iyya ba. Ya zargi jami’an jam’iyya da wasu ’yan siyasa da shirya maguɗi, tsoratarwa da hana magoya bayansa kaɗa ƙuri’a.

“A wasu mazaɓu an hana mutanenmu kaɗa ƙuri’a, an tsoratar da su har ma an kore su da ƙarfi,” inji Adelabu ga manema labarai. Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Femi Awogboro, ya ce har yanzu ba su ga wani sakamako na hukuma ba.

A jihar Gombe kuwa, tsohon Ministan Sufuri Sa’idu Alkali ya kasa samun tikitin gwamna bayan ya kaurace wa zaɓen fidda gwani bisa zargin rashin gaskiya da adalci. Zaɓen dai ya bai wa Jamilu Gwamna nasara, wanda ake ganin yana da goyon bayan Gwamna Inuwa Yahaya.

Tun kafin zaɓen, Alkali ya nesanta kansa daga tsarin, yana cewa babu gaskiya ko haɗin kai a cikinsa. Matakin nasa ya haifar da jita-jitar cewa ya janye daga takarar ko kuma yana shirin ficewa daga APC. Sai dai mai taimaka masa Umar Alkali ya musanta hakan, yana cewa tsohon ministan yana nan daram cikin takarar kuma bai fice daga jam’iyyar ba.

Makomar Tuggar na cikin tsaka mai wuya:

Yayin da wasu suka samu tikiti wasu kuma suka ƙalubalanci sakamakon zaɓe, makomar Yusuf Tuggar har yanzu tana cikin rashin tabbas. Tsohon Ministan Harkokin Waje ya yi murabus domin neman tikitin gwamnan APC a Bauchi, amma har yanzu ana cigaba da lissafin siyasa da shirye-shiryen cikin gida game da takararsa.

Abubuwan da suka faru da waɗannan tsofaffin ministoci sun sake nuna wata gaskiya a siyasar Nijeriya — riƙe babban muƙami a gwamnatin tarayya ba ya nufin mutum zai mallaki siyasar jiha ko kuma tsarin jam’iyya a matakin ƙasa.

Ga yawancin tsofaffin ministocin, yin murabus daga Majalisar Zartarwa ta Tarayya ana tsammanin zai buɗe musu hanya mai sauƙi zuwa siyasa. Sai dai zaɓen fidda gwani ya bayyana rabuwar kai, adawar cikin gida da kuma ƙorafe-ƙorafe kan yadda aka gudanar da zaɓukan APC.

A jihohi da dama, an ci gaba da zargin maguɗi, ƙaƙaba ’yan takara, tsoratar da wakilai da kuma rashin gaskiya a zaɓukan fidda gwani na jam’iyyar. Masana siyasa na ganin cewa abubuwan da suka faru da tsofaffin ministocin Tinubu na iya zama wata alama ta irin tsananin rikicin siyasa, sauyin ƙawance da fafatawar cikin gida da za su mamaye siyasar Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi