Nijeriya ta fuskanci garkuwa miliyan 2.2 da kuɗin fansa tiriliyan N2.2 a shekara – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani babban masani kan harkokin tsaro, Farfesa Oyesoji Aremu, ya bayyana cewa Nijeriya ta fuskanci mummunar matsalar tsaro inda aka kiyasta an yi garkuwa da mutane kusan miliyan 2.2, tare da biyan kuɗin fansa da ya kai kusan Naira tiriliyan 2.2 cikin shekara guda.

Farfesa Aremu ya bayyana hakan ne yayin wani babban taron lacca da ƙungiyar Caliban Kimiyyar Zamantakewa (Social Sciences Students’ Association – SOSSA) ta Jami’ar Adekunle Ajasin, Jihar Ondo, ta shirya, inda ya yi cikakken bayani kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya, matsayinta a jerin ƙasashen duniya, da kuma mummunan tasirin da rashin tsaro ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki.

Masanin, wanda ke koyarwa a Jami’ar Ibadan kuma a halin yanzu shi ne Muƙaddashin Shugaban Jami’ar Achievers, Owo, ya bayyana cewa matsalar tsaron Nijeriya ta rikiɗe zuwa abin da ya kira “tattalin arzikin biya kuɗin fansa,” wanda ke gudana ta hannun ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya dogara da bayanan da aka ce sun fito daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) a watan Disamba 2024, inda ya gargaɗi cewa matsalar tsaro ta zama kasuwanci mai hatsari da ke lalata rayuka, al’umma da tattalin arziki.

A cewarsa, yawaitar garkuwa da mutane da biyan kuɗin fansa na nuna yadda ƙungiyoyin laifi suka samu wurin zama sosai a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, rashin tsaro ba kawai yana halaka rayuka ba ne, har ma yana rage kwarin gwiwar jama’a ga gwamnati tare da tauye ƙarfin tattalin arziki da jawo koma-baya ga ci gaban ƙasa.

Farfesa Aremu ya kuma ja hankali kan matsayen Nijeriya a jerin ƙasashen duniya dangane da tsaro da bin doka. Ya ce Nijeriya na matsayi na 142 daga cikin ƙasashe 143 a World Justice Project Rule of Law Indeɗ, da kuma 148 daga 163 a Global Peace Indeɗ, sannan ta zo ta biyar a duniya a Global Terrorism Indeɗ.

Ya bayyana cewa waɗannan alƙaluma na nuna yadda tsaro da shugabanci ke ci gaba da raguwa, wanda ke shafar ci gaban ƙasa da jawo rashin amincewar masu zuba jari.

Masanin ya danganta tushen matsalar tsaro da abubuwan tarihi da suka haɗa da Yaƙin Basasa na Nijeriya, tashin hankalin Maitatsine, rikicin Neja Delta, da kuma tasowar Boko Haram.

Ya ce rashin ɗaukar matakan gaggawa a lokacin farkon bayyanar matsalolin ne ya ƙara ta’azzara rikicin da ake ciki yanzu.

Haka kuma, ya bayyana cewa rabuwar ƙungiyoyin ISWAP da sauran ƙingiyoyin tsageru, tare da yawaitar ’yan bindiga da masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, sun ƙara dagula matsalar tsaro a ƙasar.

Farfesa Aremu ya nuna damuwa kan yadda dazuzzuka masu faɗi ke zama mafakar masu laifi, inda ya ambaci Dajin Sambisa, Alagarno, Kamuku, Kuyambana, Kuduru da Old Oyo National Park a matsayin wuraren da ke zama mafaka ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Ya ce hakan na nuna ƙarancin ikon gwamnati a yankunan karkara da rashin isasshen tsaro.

Haka kuma, ya kawo batun yawaitar kai hare-hare kan makarantu a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Chibok, Dapchi, Kagara, Greenfield da wasu yankunan Jihar Oyo. Ya ce, wannan na nuna gazawa wajen tattara bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Masanin ya kuma koka kan rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, yana mai cewa akwai “ƙarar juna” maimakon aiki tare. Don magance matsalar, ya bayar da shawarar kafa ’yan sandan jiha, ƙarfafa tattara bayanan al’umma, haɗin gwiwar hukumomin tsaro, da kuma tura masu tsaron dazuka domin kare yankunan da ba su da tsaro.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar Adekunle Ajasin, Farfesa Olugbenga Ige, wanda Farfesa Adebisi Daramola ya wakilta, ya bayyana laccar a matsayin mai muhimmanci kuma ta zo a kan lokaci. Haka kuma, Farfesa Adesuyi Adebukola, ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da masana domin shawo kan matsalar.

By ukarofi