Shirin CNG na Shugaban ƙasa zai faɗaɗa tallafin sufuri a manyan makarantu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Shirin Motocin Iskar Gas da Motocin Lantarki ta Fadar Shugaban ƙasa, wato Presidential Initiative on Compressed Natural Gas and Electric Vehicles (Pi-CNG), Ismail Ahmed, ya bayyana cewa shirin na ci gaba da faɗaɗa tallafin sufuri zuwa manyan makarantu mallakin Gwamnatin Tarayya a faɗin Nijeriya.

Ahmed ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin wani taron yini guda da Asusun Lamunin Karatu na Nijeriya, wato Nigerian Education Loan Fund, ya shirya tare da shirin Pi-CNG domin wayar da kan ɗalibai. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito cewa Ofishin Kula da Ayyukan Arewa na NELFUND ne ya shirya taron.

Ahmed ya ce an ƙaddamar da shirin ne domin rage matsalolin sufuri da ɗalibai ke fuskanta a cibiyoyin karatu.

A cewarsa, tuni shirin ya kai motocin bas da kuma adaidaita sahu zuwa kusan jami’o’i 20 a sassan ƙasar nan domin sauƙaƙa zirga-zirgar ɗalibai a cikin makarantu. Ya bayyana cewa, shirin na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin tallafa wa jin daɗin ɗalibai da kuma bunƙasa harkokin ilimi.

“Yanzu haka muna aiki a kusan jami’o’i 20, kuma muna da niyyar kai wannan shiri zuwa dukkan manyan makarantu mallakin gwamnatin tarayya domin samar musu da motocin bas da adaidaita sahu domin ɗalibai su samu sauƙin zirga-zirga tsakanin wuraren karatu da sauran muhimman wurare,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, an riga an kai tallafin zuwa Jami’ar Abuja da Jami’ar Ahmadu Bello, yayin da ake shirin kaiwa Jami’ar Bayero Kano da kuma jami’ar Ibadan. Ahmed ya ce ana aiwatar da shirin ne sannu a hankali a faɗin ƙasar nan cikin tsare-tsaren tallafin gwamnatin tarayya.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta harkokin sufuri ga ɗalibai tare da tallafa wa ci gaban ilimi ta hanyar samar da hanyoyin sufuri masu sauƙi da ɗorewa.

A nasa jawabin, Manajan Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyerr, ya ce asusun ya gayyaci shugabannin ɗalibai daga jihohin Arewa 19 domin wayar musu da kai kan shirye-shiryen tallafin karatu na gwamnatin tarayya.

Sawyerr, wanda wani jami’in asusun mai suna Umar Muhktar ya wakilta, ya ce za a tattara ra’ayoyin shugabannin ɗalibai 39 da suka halarci taron kan yadda ake aiwatar da shirin lamunin karatu. A cewarsa, taron na da nufin nuna nasarorin gwamnatin Tinubu a fannin tallafin ilimi da sauran shirye-shiryen ci gaba.

“Ya zuwa yanzu, sama da ɗalibai miliyan ɗaya daga cibiyoyin ilimi daban-daban a Arewacin Nijeriya sun amfana da shirin lamunin karatu,” inji shi.

Ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Tinubu ta tabbatar da samar da isassun kuɗaɗe ga NELFUND, lamarin da ya bai wa asusun damar biyan kuɗaɗen makaranta da kuma tallafin rayuwa ga ɗalibai.

Sawyerr ya ce kasancewar an kafa dokar Majalisar Tarayya tare da samar da hukuma ta musamman domin tafiyar da shirin, hakan ya tabbatar da cewa zai ci gaba har bayan wa’adin gwamnatin yanzu. Ya kuma bayyana cewa ɗaliban da makarantunsu suka rufe rajistar zangon karatu ba za su iya neman lamunin ba sai lokacin da aka sake buɗe tsarin neman tallafin.

Shi ma Mai Kula da Ofishin Ayyukan Arewa na NELFUND, Samsudeen Ahmed, ya ce an kafa shirin ne domin tabbatar da cewa ɗaliban Arewa sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya. A cewarsa, ofishin na ci gaba da hulɗa da ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati domin tabbatar da cewa ayyukan ci gaba sun kai ga talakawa a jihohin Arewa.

By ukarofi