Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi amfani da saƙonsa na barka da sallah wajen sake jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da gwamnatinsa ta aiwatar, duk da wahalar da suka jawo, sun zama dole kuma yanzu sun fara haifar da ɗa mai ido.
Musulman a Nijeriya kamar takwarorinsu a faɗin duniya za su gudanar da bikin sallar Idi da aka fi sani da babbar sallah a ranar Laraba.
A cikin saƙonsa na a ranar Talata na taya al’umma murnar bikin sallah, shugaba Tinubu ya ce:
“Sauye-sauyen da muka aiwatar suna da wahala, amma sun zama dole domin gina Nijeriya da bunƙasar tattalin arziƙin al’umma masu zuwa.
“Kamar yadda sadaukarwa ke haifar da sakamako, ina farin cikin cewa sadaukarwa da ƙoƙarin da muka yi cikin shekaru uku da suka gabata sun samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa wanda ya sanya ƙasarmu ta zama wurin da masu zuba jari suke rige-rigen zuwa wanda hakan zai samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikinmu. Duhun da muke fama da ita ta ƙare, haske ya bayyana.”
Manhaja ta ruwaito cewa daga cikin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo akwai cire tallafin man fetur da kuma samar da tsayayyen farashin musayar kuɗin waje. Waɗannan manufofi sun jawo tsadar rayuwa ga miliyoyin ‘yan Nijeriya, amma kuma sun jawo wa gwamnati tiriliyoyin kuɗi waɗanda aka mayar da su fannoni kamar lafiya da ilimi tare da taimakawa wajen daidaita darajar Naira.
Shugaban ƙasa ya amince cewa akwai matsalar rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, wadda ta yi sanadin rasa rayukan dubban mutane da garkuwa da wasu da dama.
“Ina sane cewa duk da ƙoƙarin jami’an tsaro da hukumomin leƙen asiri ke yi — ciki har da kashe wani shugaban ISIS da ake nema ruwa a jallo kwanan nan — sai dai har yanzu ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga na kai hare-hare kan al’umma. Ina tabbatar muku cewa kuna raina ban a manta da ku ba. A ƙarshe za mu yi nasara a kan dukkan miyagun mutanen nan,” ya faɗa.
Ga cikakken saƙon shugaba Tinubu:
“Ina miƙa sakon taya murna ga ‘yan’uwa Musulmi a Nijeriya da faɗin duniya yayin da suke bikin sallah, wato bikin sadaukarwa.
Muna gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da Ya raya mu har muka sake ganin wannan sallah.
Sallah na tuna mana da kyawawan halayen Annabi Ibrahim — imani, biyayya da kuma shirinsa na sadaukarwa saboda manufa mafi girma. Wannan biki mai tsarki na kira ga dukkan Musulmi har ma da dukkan ‘yan Nijeriya da al’ummar duniya bakiɗaya da su rungumi sadaukarwa, tausayi, haɗin kai da jinƙai ga juna.
ɗaya daga cikin manyan darussan ranar Sallar shi ne nuna rahama da tausayi ba tare da la’akari da ƙabila, launin fata ko addini ba. Babu wani misali mafi girma na biyayya da sadaukarwa da ta kai ta Annabi Ibrahim wanda ya amince ya sadaukar da ɗansa guda ɗaya, Isma’il.
A matsayinmu na ƙasa, muna kan tafarkin sake gina Nijeriya da sabunta ta. Sauye-sauyen da muka aiwatar suna da wahala amma sun zama dole domin gina ƙasa mai ƙarfi da wadatar arziƙi ga kowa.
Kamar yadda sadaukarwa ke kawo sakamako, ina farin cikin sanar da ku cewa sadaukarwa da ƙoƙarin da muka yi cikin shekaru uku da suka gabata sun samar da cigaban tattalin arziki mai ɗorewa wanda ya sanya ƙasarmu ta zama wurin da masu zuba jari suka fi so, lamarin da zai samar da ayyukan yi da bunƙasar tattalin arziki. Magaar duhu ya ƙare, haske ya bayyana.
Ina da yaƙinin cewa da yardar Allah, sauye-sauyen da muka aiwatar da jajircewa za su ci gaba da samar da ingantaccen tsaro da ƙarin damarmaki ga kowa.
Ina sane cewa duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro da hukumomin leƙen asiri ke yi — ciki har da kashe wani shugaban ISIS da ake nema ruwa a jallo kwanan nan — har yanzu ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga na cigaba da kai hare-hare kan al’umma. Ina tabbatar muku cewa ban manta da ku ba. A ƙarshe za mu yi nasara a kan dukkan miyagun mutanen.
Ga ‘yan’uwa Musulmi, ina roƙon ku da ku yi amfani da wannan lokaci mai albarka wajen yi wa ƙasarmu addu’a, domin samun zaman lafiya a cikin al’ummominmu da kuma kyakkyawan shugabanci.
Muna addu’ar cewa masu aikata laifuka a tsakaninmu za su tuba su daina miyagun ayyukansu ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri bisa tanadin doka.
Haka kuma ya kamata mu taimaki wa marasa galihu, mu sada farin ciki ga maƙwabtanmu, tare da ƙarfafa zumuncin da ke haɗa mu waje ɗaya a matsayin al’umma ɗaya.
Gwamnatina na ci gaba da jajircewa wajen gina Nijeriya inda dukkan ‘yan ƙasa za su rayu cikin zaman lafiya, su yi addininsu cikin ‘yanci, kuma su cika burinsu ba tare da tsoro ba.
Za mu ci gaba da zuba jari a fannin tsaro, samar da ababen more rayuwa, noma da bunƙasa rayuwar jama’a domin cika babban alƙawarin da muka yi wa ƙasarmu.
A madadin gwamnatina, ina yi muku fatan yin sallah lafiya, samun farin ciki da albarka. Allah Ya karɓi ibadunmu da sadaukarwarmu. Allah ya yi wa Nijeriya albarka.
