Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hamisu Mailantarki da Usman Garry, sun yi watsi da ayyana Isa Ali Pantami a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar, suna mai bayyana matakin a matsayin “wasan siyasa” da kuma rashin adalci.
A tarukan manema labarai daban-daban da suka gudanar, Mailantarki da Garry sun nuna rashin amincewarsu da yadda aka tabbatar da Pantami a matsayin dan takarar gwamna na bangaren PDP mai alaka da Ministan Abuja, Nyesom Wike, domin zaben 2027.
Pantami ya samu tikitin ne jim kadan bayan sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki, bayan da ya zargi shugabancin APC a jihar Gombe da yi masa rashin adalci.
Mailantarki ya tambayi sahihancin yadda Pantami ya samu tikitin, yana zargin cewa tsohon ministan sadarwar bai dade da barin APC ba kuma bai shiga tsarin neman tikitin gwamna na PDP yadda ya kamata ba.
Ya yi zargin cewa Pantami ya ziyarci wani jigo na jam’iyyar cikin dare, sannan washegari aka bayyana shi a matsayin dan takarar gwamna.
A cewarsa, hakan ya saba da tsoffin kalaman Pantami na yaki da rashin adalci.
“Shi ne wanda ya taba cewa zai yaki rashin adalci har zuwa digon jininsa na karshe, amma yau ga shi ya shigo jam’iyyarmu ya amince da tikitin da aka samar ta hanyar rashin adalci,” in ji Mailantarki.
Ya ƙara da cewa mutum hudu ne kacal suka sayi fom din takara tare da shiga tantancewar jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, kuma Pantami bai kasance cikin su ba.
Mailantarki ya ce an yi watsi da masu biyayya ga jam’iyyar da suka bi ka’ida, yana gargadin cewa irin wannan mataki na iya haddasa rikici da rabuwar kai a PDP a jihar Gombe.
Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar su tabbatar da adalci, gaskiya da dimokuradiyya ta cikin gida, yana mai cewa bai kamata a yi watsi da ra’ayin ‘yan jam’iyya na hakika da masu neman takara ba.
Garry ya ce an gudanar da “wasan Kwaikwayo ne ba tsaida dan takara ba”
Shi ma Usman Garry ya soki tsarin da ya bai wa Pantami tikitin takarar gwamna.
Garry, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Kogunan Gombe, ya ce har yanzu yana jiran kammala tsarin zaben a hukumance a ranar Talata, yana mai cewa babu daya daga cikin ‘yan takara hudu da aka tantance da aka tuntuba kafin ayyana Pantami.
Ya buƙaci shugabannin PDP da sauran masu ruwa da tsaki su yi watsi da abin da ya kira “wasa” da aka gudanar, sannan su koma ga yarjejeniyar da ‘yan takarar suka cimma tun farko.
Rikicin cikin gida da ya biyo bayan ayyana Pantami na kara nuna rarrabuwar kawuna a cikin PDP a jihar Gombe yayin da jam’iyyar ke kokarin tunkarar zaben 2027.
