Remi Tinubu ta buƙaci a dakatar da auren yara mata da wuri domin daƙile matsalar ciwon yoyon fitsari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Oluremi Tinubu ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su ƙara ƙaimi wajen inganta lafiyar mata tare da dakatar da aurar da yara mata da wuri domin rage matsalar yoyon fitsari.

Ta bayyana hakan ne yayin bikin ranar Yoyon Fitsari ta Duniya, inda ta jaddada cewa bai kamata mace ta ci gaba da fama da matsalar da za a iya kauce wa ko kuma a magance ta cikin sauƙi ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Oluremi Tinubu ta bayyana yoyon fitsari a matsayin matsala da ke sa fitsari ko bahaya na fita daga jikin mace ba tare da saninta ba, galibi sakamakon doguwar naƙuda yayin haihuwa ba tare da samun kulawar da ta dace ba.

Ta ce matsalar na haddasa wa mata cututtuka, lalacewar jijiyoyin gabobin haihuwa da kuma tsangwama daga al’umma saboda wariya da ƙyama.

Jami’an lafiya sun bayyana cewa yoyon fitsari kan faru ne idan mace ta yi doguwar nakuda yayin haihuwa, musamman idan kwankwason mace bai isa haihuwa ba ko kuma jaririn bai zauna yadda ya kamata a mahaifa ba.

Sun ce idan ba a samu kulawar kwararrun jami’an lafiya cikin gaggawa ba, matsalar kan janyo illa ga mahaifa tare da haddasa mutuwar jariri.

Masana sun ƙara da cewa matsalar ta fi shafar mata talakawa, yara mata masu ƙarancin shekaru da kuma matan da suka yi haihuwa a gida ba tare da kulawar likitoci ko ma’aikatan lafiya ba.

Ana gudanar da ranar Yoyon Fitsari ta Duniya ne a duk ranar 23 ga watan Mayu domin wayar da kan jama’a game da hadarin da matsalar ke haifarwa ga mata tare da karfafa samar da kulawa ga wadanda suka kamu da ita.

Taken bikin bana shi ne: “Lafiyarta, Hakinta: Kawar da yoyon fitsari domin inganta rayuwar mata.”

Oluremi Tinubu ta jaddada cewa samun ingantacciyar lafiya hakki ne na kowace mace da yarinya.

Ta ce aurar da yara mata da wuri da kuma daukar ciki kafin jikin yarinya ya gama girma na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa yoyon fitsari.

Haka kuma ta ce al’adun gargajiya masu cutarwa, talauci da rashin ilimi na hana mata samun ingantattun bayanai da kulawar lafiya musamman kan haihuwa.

Uwar gidan shugaban kasar ta yi kira ga gwamnati, iyaye da shugabannin al’umma da su hada hannu wajen dakatar da auren yara mata, karfafa mata ta hanyar koyar da sana’o’i, samar musu ilimin zamani da na addini da kuma inganta harkokin kiwon lafiya.

Bincike ya nuna cewa Nijeriya na daga cikin kasashen da ke da yawan mata masu fama da yoyon fitsari, inda ake samun dubban sababbin masu dauke da matsalar duk shekara.

Rahotanni sun nuna cewa ana samun karin mata kusan 13,000 da ke kamuwa da matsalar a duk shekara, yayin da sama da mata 400,000 ke bukatar tiyata domin magance matsalar.

Masana sun bayyana cewa matsalar ta fi kamari a Arewacin Nijeriya saboda talauci, rashin ingantattun cibiyoyin lafiya, aurar da yara mata da wuri da kuma haihuwa a gida.

Sun kuma ce doguwar nakuda na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa haihuwar jarirai ba tare da rai ba.

By ukarofi