NAHCON ta murza gashin baki kan ingancin abinci da tura alhazai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da jin daɗi da kare lafiyar alhazai, inda ta sanar da ɗaukar tsauraran matakai kan ingancin abincin da ake bai wa alhazai a aikin hajjin wannnan shekara ta 2026.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da dokoki da ƙa’idojin lafiya da kula da abinci da ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa domin tabbatar da kare lafiyar alhazai, musamman duba da yanayin zafin da ake fama da shi a lokacin aikin hajji.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta ce an ƙi karɓar wasu abincin dare da aka tanada wa alhazai ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2026, bayan an gano cewa ba su cika ƙa’idojin da suka shafi yadda ake sarrafa abinci da kuma yadda ake tattara shi ba.

NAHCON ta ce an ɗauki matakin ne tare da haɗin gwiwar hukumomin lafiya na Saudiyya domin kauce wa duk wata matsalar lafiya da ka iya shafar mahajjatan Nijeriya.

Hukumar ta ƙara da cewa nan take aka samar wa alhazan da abin ya shafa wasu kayan sha da abinci masu sauƙi domin tabbatar da cewa ba a samu tangarɗa ga walwalarsu ba.

Mambobin kwamitin gudanarwar hukumar sun kuma yi wa shugabannin alhazai na jihohi bayani kan halin da ake ciki, yayin da shugaban hukumar, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya umurci Kwamitin Tsaro da ya gudanar da bincike kan masu samar da abincin da duk masu ruwa da tsaki da ke da alaƙa da kwangilar.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa ana ci gaba da shirye-shiryen mayar wa mahajjatan da abin ya shafa kuɗinsu cikin gaggawa.

A wani ci gaban kuma, Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta sanar da fara gudanar da bincike kan wasu kamfanonin shirya aikin Hajji da ake zargi da tura ƙarin alhazai fiye da adadin da aka amince musu da shi a aikin Hajjin shekarar 2026 da ake gudanarwa a ƙasar Saudiyya.

Hukumar ta bayyana cewa ana kuma binciken wasu daga cikin kamfanonin ne bisa zargin cin moriyar wasu alhazai tare da muzanta musu haƙƙoƙinsu yayin gudanar da ibadar Hajji a ƙasa mai tsarki.

Shugaban Hukumar NAHCON, Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya umarci Babban Kwamitin Tsaro na hukumar da ya gano kamfanonin da ke da hannu a lamarin tare da gudanar da cikakken bincike kan yadda aka karya ƙa’idojin aikin Hajji.

A cewar hukumar, duk wani kamfani da aka samu da laifi bayan kammala bincike zai fuskanci hukunci mai tsauri, har da yiwuwar soke lasisin gudanar da aikin Hajji da aka ba shi.

NAHCON ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da bin ƙa’idojin gudanar da aikin Hajji tare da kare walwala da muradun mahajjatan Nijeriya da ke Saudiyya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Saudiyya suka ƙara tsaurara sa ido kan zirga-zirgar alhazai, masaukinsu da walwalarsu yayin da aikin Hajji ke ƙara ƙaratowa ga muhimman ranaku.

A wani ɓangaren kuma, hukumar ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da ingancin abinci da lafiyar mahajjata bayan da aka ƙi karɓar wasu abincin dare da aka tanada ranar 27 ga watan Mayu saboda rashin cika ƙa’idojin sarrafa abinci da tattarawa da hukumomin lafiya na Saudiyya suka gindaya.

Hukumar ta ce nan take aka janye abincin tare da haɗin gwiwar jami’an lafiya na Saudiyya domin kauce wa duk wata matsalar lafiya da ka iya tasowa ga mahajjata.

Sai dai NAHCON ta tabbatar da cewa an gaggauta samar wa mahajjatan da abin ya shafa wasu kayan shaye-shaye da abinci masu sauƙi kafin a kammala wasu sababbin tsare-tsare.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa an soma shirye-shiryen mayar da kuɗi ga alhazan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa za ta ci gaba da kare jin daɗinsu da tsaronsu a duk tsawon aikin Hajjin 2026.

NAHCON ta kuma jaddada cewa wajibi ne duk masu ruwa da tsaki a harkar Hajji su bi ƙa’idoji da matakan da aka shimfiɗa domin tabbatar da gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali ga alhazan Nijeriya.

By ukarofi