Zaɓen fidda gwanin ADC: Magoya bayan El-Rufai na zargin an yaudare su

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rikicin cikin gida na ci gaba da ƙamari a jam’iyyar ADC reshen Jihar Kaduna, yayin da wasu daga cikin magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ke zargin sa da yin watsi da tsarin siyasar da ya tsaya masa tsayin daka tsawon shekaru.

Abin da ya fara a matsayin saɓani kan zaɓen fidda gwani na kujerar gwamna da na ’yan majalisa yanzu ya rikiɗe zuwa babbar ɓaraka a cikin jam’iyyar, inda masu biyayya ga El-Rufai ke zargin cewa an yi watsi da biyayyarsu da sadaukarwar da suka yi ta hanyar yarjejeniyoyin sirri da kuma amfani da wakilai wajen cimma muradun siyasa.

Rikicin ya ƙara ɗaukar zafi ne bayan da Isa Ashiru Kudan ya fito a matsayin ɗan takarar gwamna na ADC a jihar Kaduna, sakamakon da wasu ’yan takara da jiga-jigan jam’iyyar suka ce ba su amince da yadda aka gudanar da zaɓen ba.

Daya daga cikin fitattun masu neman takarar gwamna, Alhaji Ja’afaru Sani, wanda ake ganin na hannun daman Malam Nasir El-Rufai ne, ya fito fili ya yi watsi da sakamakon zaɓen, yana mai bayyana shi a matsayin maguɗi tare da yin barazanar ficewa daga jam’iyyar idan ba a yi masa adalci ba.

Matsayar tasa ta haddasa ƙarin bore daga masu neman takarar ‘yan majalisa da sauran magoya bayan tsohon gwamnan. Wata ƙungiya ƙarƙashin jagorancin Samaila Makarfi ma ta bayyana zaɓen a matsayin “wasan kwaikwayo”, tana zargin an tafka maguɗi da murɗe sakamako tare da yunƙurin danne wasu ɓangarori a cikin jam’iyyar.

Sai dai baya ga rikicin sakamakon zaɓen, wasu daga cikin masu korafin sun bayyana cewa babban abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya shi ne yadda suke ganin El-Rufai ya yi watsi da wazanda suka tsaya masa a lokutan ƙalubale na siyasa da na shari’a.

Wasu majiyoyi daga cikin ɓangaren sun bayyana cewa magoya bayan na jin an barsu cikin duhu, duk da irin haɗarin siyasa da suka ɗauka domin kare martabar El-Rufai.

Ana ganin fushin ya fi ƙarfi musamman dangane da batun Ja’afaru Sani, wanda ake zargin hukumomin yaƙi da cin hanci suna bincikensa, da kuma tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Bashir Saidu, wanda ke tsare a gidan gyaran hali na Kaduna.

Majiyoyi sun ce da dama daga cikin magoya bayan El-Rufai sun yi tsammanin zai tsaya musu kai da fata, amma yanzu suna ganin muradun siyasa da na kashin kai sun fi fifiko kan biyayya da gwagwarmayar da suka yi tare.

An kuma ƙara samun ƙorafi bayan zargin cewa wasu wakilan siyasa masu alaƙa da El-Rufai sun taka rawa a ɓoye wajen tabbatar da nasarar Isa Ashiru, duk kuwa da cewa a fili an ce tsohon gwamnan bai goyi bayan kowane ɗan takara ba.

Rahotanni sun ce matar El-Rufai, Asiya El-Rufai, ta gana da wasu masu neman takara domin tabbatar musu da cewa mijinta bai marawa kowa baya ba, amma hakan bai rage zafin rikicin ba.

Wasu daga cikin masu biyayya ga El-Rufai sun dage cewa sakamakon zaɓen ya nuna akwai wata yarjejeniya ta siyasa da aka shirya tun farko domin fifita wasu tare da jefa tsofaffin magoya baya cikin ƙunci.

Haka kuma, wasu masu ruwa da tsaki sun zargi tsohon gwamnan da mayar da hankali kan makomar siyasar ɗansa, Bello El-Rufai, yayin da waɗanda suka taimaka wajen gina da kare tsarin siyasarsa aka bar su babu kariya.

Rikicin ya ƙara tsananta ne saboda rashin ikon El-Rufai na sa baki kai tsaye sakamakon tsare shi da ake yi daga hukumar ICPC, lamarin da wasu ke ganin ya haifar da gibin jagoranci da wasu ɓangarori ke amfani da shi.

A halin yanzu dai shugabancin ADC a Kaduna ya rabu gida biyu. Kafin gudanar da zaɓen fidda gwani, jam’iyyar ta nesanta kanta daga wani taron “Kwamitin Riƙon ƙwarya na ADC” da ake danganta shi da magoya bayan El-Rufai, wanda rahotanni suka ce ya rikiɗe zuwa tashin hankali da harbe-harbe, lamarin da ‘yan sanda ke bincike a kai.

Masu lura da al’amuran siyasa na gargaɗin cewa idan ba a shawo kan rikicin ba, jam’iyyar ADC a Kaduna na iya fuskantar babbar tsaga gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi