’Yan bindiga sun ƙona fadar sarki da sace mata da yara a Kwara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari mummunan hari da tsakar dare a garin Yashikira da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara, inda suka kai farmaki ofishin ‘yansanda da kuma fadar Sarkin Yashikira tare da kona wani bangare na fadar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 2:00 na dare ranar Litinin, inda suka rika harbe-harbe wanda ya jefa mazauna yankin cikin firgici tare da sa mutane guduwa zuwa dazuka domin tsira.

An bayyana cewa maharan sun sace kimanin mutum 10, ciki har da wasu mata da yara, yayin da Sarkin Yashikira ya tsallake rijiya da baya ba tare da ya samu rauni ba.

Shugaban karamar hukumar Baruten, Issa Jubril, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa sarkin na cikin koshin lafiya duk da cewa an sace wasu daga cikin mutanen da ke cikin fadar.

Shi ma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da harin, yana mai cewa kwamishinan ‘yan sanda ya umarci fara wani samame na musamman tare da hadin gwiwar sojoji, masu gadin dazuka da kungiyoyin sa-kai domin ceto wadanda aka sace da kuma kamo maharan.

Rundunar ta ce an kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke fama da barazanar hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

By ukarofi