’Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan tara wajen sayen kati da data a 2025 – Rahoto

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rahoto ya nuna cewa kwastomomin manyan kamfanonin sadarwa guda huɗu a Najeriya sun kashe kusan Naira tiriliyan 9 wajen sayen kati da data a shekarar 2025, lamarin da ya ƙara yawan kuɗaɗen shiga na kamfanonin.

Kamfanin MTN  ya samu sama da Naira tiriliyan 5.3 daga kwastomomi miliyan 90.3, inda ya koma samun riba bayan haraji ta Naira tiriliyan 1.11. Haka kuma Airtel ya samu kusan Naira tiriliyan 3.1 daga kwastomominasa miliyan 60.9.

Rahoton ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga ya samo asali ne daga ƙaruwar amfani da data, yawaitar amfani da wayoyin zamani da kuma ƙarin kuɗin kuɗaɗen sadarwa da Hukumar NCC ta amince da shi.

An bayyana cewa matsakaicin kuɗin da kowane kwastoma ke kashewa a MTN ya kai Naira 5,184 a wata a shekarar 2025, yayin da na Airtel ya kai Naira 3,326.

Kamfanonin sun kuma samu ƙarin masu amfani da data, inda amfani da intanet ya ƙaru sosai a faɗin ƙasar. Hukumar NCC ta ce ’yan Najeriya na amfani da kusan terabyte 45,800 na data a kullum a shekarar 2026, idan aka kwatanta da terabyte 32,100 a shekarar da ta gabata.

Sai dai masu amfani da layukan sadarwa sun koka kan cewa duk da yawan kuɗin da suke kashewa, har yanzu ana fama da matsalar rashin network a wasu wurare.

By ukarofi