Kwalara ta kashe mutum 27 a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Aƙalla mutum 27 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a wasu ƙananan hukumomi shida na Jihar Borno, yayin da aka samu mutum 2,715 da ake zargin sun kamu da cutar cikin kwanaki 24 na farkon watan Mayu.

Rahoton da aka samu ya nuna cewa cutar ta ɓarke a ƙananan hukumomin Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri, inda birnin Maiduguri ya kasance cibiyar da cutar ta fi ƙamari da mutum 1,568 da ake zargi sun kamu.

Rahoton ya ce annobar na ƙara tsananta, yayin da ake ci gaba da samun sabbin masu ɗauke da cutar a sassa daban-daban na jihar.

An kuma bayyana cewa mutum 11 daga cikin mamatan sun mutu ne a cikin al’umma sakamakon jinkirin samun kulawar lafiya, yayin da wasu 16 suka mutu a cibiyoyin kiwon lafiya.

Ma’aikatan lafiya sun nuna damuwa kan jinkirin ayyana dokar ta-ɓaci kan lafiyar jama’a da kuma rashin ƙaddamar da gangamin wayar da kai kan cutar.

Sai dai Daraktan Lafiyar Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Borno, Dakta Goni Imam Ali, ya ce ba daga wurinsu wannan rahoton ya fito ba, amma kuma ya ƙi yin ƙarin bayani kan lamarin.

By ukarofi