Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Ondo, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ceto ɗalibai da malamai da ’yan ta’adda suka sace a Oyo.
Gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ne, ya bayyana hakan ta bakin mataimakinsa da ya wakilce shi a bikin Ranar Yara ta ƙasa da aka gudanar a jihar.
Ya kuma jaddada ƙoƙarin gwamnatin wajen samar da manufofi da tsare-tsare domin walwalar yara ƙanana, da kuma hana bautar da su.
Hakazalika, ya ce bikin ba zai tsaya a iya gudanar da taro ba kawai, zai ninka ƙoƙari wajen kare rayukansu, da inganta fannin ilimi da ci gaban kowane yaro da ke Jihar Ondo da Nijeriya baki ɗaya.
“Tsawon shekaru da dama mu ke biya wa ɗaliban sakandare kuɗin jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NABTEB, domin tabbatar da ’ya’yan masu ƙaramin ƙarfi sun samu ilimin da ya kamata.”
Ita ma kwamishinar mata ta jihar, Seun Osamaye, ta ce gwamnatin na iya bakin ƙoƙarinta domin ganin an samu ragi a yawan ƙididdigar bautar da yara, cin zarafinsu, da kuma safarar su a ciki da wajen jihar.
Ita ma mai ɗakin gwamnan jihar, Oluwaseun Aiyedatiwa, ta yi kira da al’umma su yawaita addu’a da kuma bayar da goyon bayansu ga ƙananan yara da malaman da aka sace a Jihar Oyo.
