Sojoji sun ceto mutum 92 a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sojojin Nijeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai OPHK’ dake aikin samar da tsaro a Arewa maso Gabas sun ceto mutum 92 daga hannun mahara da suke zargin Boko Haram ko kungiyar ISWAP a hanyar Buratai zuwa Kamuya dake karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Kakakin rundunar Sani Uba ya sanar da haka a wani takarda da ya fitar inda yake cewa jami’an tsaron rundunar ‘135 special Forces Battalion’ dake Dutse Kura suka samu bayanin cewa mahara sun tasa keyar mutane matafiya daga cikin motocin su a titi zuwa cikin daji da misalin karfe 11:22 na safe.

Ya ce jami’an tsaron sun tattaro wannan bayanan ne bayan tsananta bincike.

Uba ya ce jami’an tsaron na tabbatar da haka ne sojojin rundunar ‘135 special Forces Battalion’ da na rundunar 27 Task Force Brigade Garrison suka hadu domin ceto mutanen.

Ya ce jami’an tsaron sun fatattaki maharan har zuwa Mangari zuwa Dora inda a nan suka yi batakashi da maharan har suka samu nasarar ceto mutanen bayan maharan sun gudu.

”Daga cikin mutum 92 din da aka ceto akwai maza 52, mata 33 da yara bakwai tare da kwato ababen hawa 8.

Uba ya ce maharan sun dasa bamabamai a hanyoyin Bula Zarma, Mangari domin hana maharan ci gaba da fatattakan su.

“Wannan mataki da maharan suka dauka bai ci nasara ba domin fannin jami’an tsaron da suka kware wajen chanchala bamabamai sun chanchala duk bamabaman.

Ya ce hakan ya taimaka wa jami’an tsaron wajen ci gaba da fatattakan maharan har zuwa wuraren Mangari.

”Jami’an tsaron sun gudanar da bincike a daji amma basu samu nasarar kama maharan ba domin duk sun gudu.

Uba ya ce babu jami’in tsaron da ya ji rauni ko ya mutu a dalilin farmakin da suka kai wa maharan.

Ya ce rundunar ta kawo jami’an lafiya domin tabbatar da lafiyar mutane da aka ceto sannan aka raka su daga wurin zuwa Damaturu inda daga nan suka karisa zuwa inda za su.

By ukarofi