
Daga BELLO A. BABAJI
Matar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Johnathan, wato Dame Patience Johnathan ta jaddada goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu wajen ganin ya samu zarcewa a zaben 2027.
Ta bayyana cewa da ita da mijin nata ba za su koma ‘Aso Rock’ ba la’akari da tarihin shugabancin ƙasar.
A lokacin da ta ke magana a wani taro da Kamfanin Accolade Dyanamics Limited ya shirya a Abuja, ranar Asabar inda aka karrama ta da kyautar gwarzuwar shekara ta mata (Women Icon Leader of the Year), Patience ta bayyana matsayarta ne a lokacin da ta ke mika godiya ga ƴar shugaban kasar, Folashade Tinubu-Ojo bisa gudumawarta acikin al’umma.
Ta bayyana shugabancin Nijeriya a matsayin abinda ake yi daga wane zuwa wane, inda ta ke ganin goyon bayan Shugaba Tinubu shi ne daidai a yanzu.
Matar tsohon shugaban ƙasar ta kuma ce, akwai alaka mai karfin a tsakanin ta da matar Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu tun tsawon lokaci kafin mazajensu su jagoranci Nijeriya, inda a saboda haka ne ta ce ba ta shirya koma wa Villa ba.
Ta kara da cewa, a yanzu abinda ya fi dacewa shi ne ta mara wa kawarta baya wajen ganin sun yi nasara a zaben 2027, ta na mai cewa ta gamsu da hakan a matsayin abinda ke sanya ta farin ciki.
Haka kuma, ta yi godiya ga dauakcin ƴan uwanta mata bisa goyon bayanta da suka yi wanda hakan ya kai ga ta samu nasarar lashe kyautar, ta na mai kira ga majalisar dokoki da ta daina nuna wariya ga mata a harkokin shugabanci ganin yadda suke taka muhimmiyar rawa acikin al’umma.
